Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari yanzu haka Ngurbuwa a jihar Yobe

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari yanzu haka Ngurbuwa a jihar Yobe

Yan ta'addan Boko Haram yanzu haka na kaihari garin Ngurbawa dake karkashin karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Wannan ya biyo bayan harin da yan ta'addan suka kai garin Geidam ranar Laraba inda suka kashe mutane biyu kuma sukayi awon gaba da hakimi.

Yan ta'addan Boko Haram sun yi awon gaba da hakimi a garin Geidam inda suka kai hari suna harbin kan mai uwa da wabi ranar Laraba, 6 ga watan Junairu, 2021.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan ta'addan sun hari shaguna inda suka fasa suka kwashi kayan abinci sannan suka bankawa shagunan wuta.

Modu Ali, mazaunin garin ya bayyanawa manema labarai cewa bayan shagunan da suka yi fashin kayan masarufi kuma suka kona, sun kona gidan tsohon shugaban karamar hukumar, Dr Mulima Mato.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya sanar da yan sanda cewa sun gano konanniyar mota kirar Hilux da gawawwaki biyu ciki amma basu sani ko yan Boko Haram bane ko yan gari.

Karin bayani na nan tafe....

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari yanzu haka Ngurbuwa a jihar Yobe
Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun kai hari yanzu haka Ngurbuwa a jihar Yobe
Source: Original

Source: Legit.ng

Online view pixel