KAI TSAYE: Yadda zabukan maye gibin kujerun yan majalisu ke gudana

KAI TSAYE: Yadda zabukan maye gibin kujerun yan majalisu ke gudana

Bayan an dage zabukan har sau biyu sakamakon annobar cutar Korona da zanga-zangan EndSARS, hukumar gudanar da zaben kasa INEC zata gudanar da zabukan maye gibi 15 a yau Asabar.

Yayinda shida ciki na kujeran Sanatoci ne, tara na kujerun yan majalisan dokokin jiha ne.

KAI TSAYE: Yadda zabukan maye gibin kujerun yan majalisu ke gudana
KAI TSAYE: Yadda zabukan maye gibin kujerun yan majalisu ke gudana
Source: Twitter

INEC ta ce zaben kujeran majalisa mai wakiltan mazabar Bakura ya zama 'Inconclusive'

Hukumar shirya zabe ta INEC ta alanta zaben mazabar Bakura bai kammalu ba.

Baturen zaben, Farfesa Ibrahim Magawata, ya sanar da hakan a cibiyar tattara zaben, TVC ta ruwaito.

PDP: 18,645

APC: 16,464.

An ce zaben bai kammalu ba saboda adadin kuri'un da aka soke sun fi adadin tazarar dake tsakanin yan takaran biyu.

Jami'ar APC ta lashe zaben kujeran majalisa na mazabar Dass a jihar Bauchi

Jam'iyyar adawa a jihar Bauchi, APC, ta lashe zaben kujeran dan majalisa mai wakiltar mazabar Dass a jihar.

Tsohon Kakakin majalisa, Yakubu Dogara, ya bayyana hakan yayinda yake taya wanda yayi nasaran murna a shafinsa na Tuwita.

Jam'iyyar APC ta kashe zaben karamar hukumar Kosofe

An fara kirgan kuri'un da jama'a suka kada a rumfunan zaben mazabar Legas ta Gabas cikin lumana.

APC ta kashe karamar hukuma daya cikin biyar

Madogara: TVC News

Online view pixel