Basaraken Kogi ya alaƙanta rushe SARS da ƙaruwar ayyukan bata gari, ya bayyana yadda ya sha da kyar hannun 'yan bindiga

Basaraken Kogi ya alaƙanta rushe SARS da ƙaruwar ayyukan bata gari, ya bayyana yadda ya sha da kyar hannun 'yan bindiga

- Basarake mai daraja ta ɗaya a Jihar Kogi ya bayyana yada ya tsallake rijiya da baya yayin da ƴan bindiga suka tare motarsa

- Basaraken ya alakanta rushe rundunar SARS da ƙaruwar ayyukan ƴan bindiga, ƴan fashi da makami, da kuma yan tada kayar baya a manyan titunan ƙasar nan

- Ya roƙi gwamnati ta gaggauta samar da madadin rundunar SARS don takaita ayyukan bata gari a sassan ƙasar

Wani babban basarake a Jihar Kogi, Ohi na Adavi, mai martaba Alh. Muhammad Ireyi Bello, ya bayyana yadda ya sha da ƙyar da ya faɗa hannun ƴan bindiga a hanyar Lokoja zuwa Abuja.

A cewar basaraken, ya na kan hanyar dawowa daga addu'ar uku na rasuwar marigayi Hon. Sulaiman Kokori, da aka gudanar a Abuja lokacin da ya kusa fadawa hannun yan bindiga a kauyen Magajiya, kusa da Banda a jihar Kogi, ranar Talata 17 ga Nuwamba.

Wani basarake a Arewa ya alaƙanta rushe SARS da ƙaruwar ayyukan bata gari

Wani basarake a Arewa ya alaƙanta rushe SARS da ƙaruwar ayyukan bata gari. Hoto daga @lindaikeji
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Da ya ke jawabi ranar Juma'a 20 ga Nuwamba, ya ce mota kirar SUV da ta ke ɗauke dashi da wasu fasinjoji ta dan rage gudu ne don kauracewa wani ramin kan titi, sai kawai wasu mutane cikin shirin yaki, suka fito daga daji suka bude wuta akan motar.

Ya kuma bayyana cewa tsananin kwazon direban sa ne ya sa ya dinga dabarun kaucewa harsashi har ta kai sun kubuta ba tare da wani yaji rauni ba.

Da ya ke godewa Ubangiji da ya tserar da rayuwarsa, basaraken ya alakanta karuwar ayyukan ta'addanci, fashi da kuma garkuwa da mutane da rushe rundunar SARS da gwamnati tayi ba tare da "samar da madadin su ba".

KU KARANTA: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

"Ba a rushe tsari gaba ɗaya saboda wata ƴar karamar matsala, musamman in ba a tanadi masu maye gurbi cikin gaggawa ba," a cewar sa.

Basaraken ya roki gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar da masu maye gurbin cikin gaggawa da kuma daukar matakin karawa hukumar karfi.

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya siffanta Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin 'raɓa' a yayin da ya ke tsokaci a kan wani littafi da aka rubuta kan shugaban kasar mai taken "The Buhari in Us".

Yahaya Bello ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a shafunkan sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel