An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata

An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata

- An kama wasu samari 2 da ake zargin 'yan damfara ne da akwatin gawa cike da 'yan kamfan mata da rigunan nono a jihar Delta

- 'Yan sa kai ne suka fara kama samarin tukunna aka sanar da hukumar 'yan sanda, wadanda suka yi gaggawar zuwa

- In ban da hukuma ta iso da wuri, da tuni mutane sun kashe samarin wadanda ake zargin matsafa ne

Wasu 'yan sanda da 'yan sa kai da ke Ogwashi-Uku, karamar hukumar Aniocha ta kudu da ke jihar Delta, sun kama wasu samari 2 da akwatin gawa, cike da 'yan kamfan mata da rigunan nono.

An kama wadanda ake zargin a wuraren Agidiehe quarters da misalin karfe 9:30 na daren Laraba, kamar yadda labarai suka bayyana.

Sai da 'yan sa kai suka kama su tukunna aka sanar da 'yan sanda. Kamar yadda wata majiya ta sanar, hankulan mata da samarin yankin sun yi matukar tashi sakamakon aika-aikan 'yan damfarar yanar gizon.

Kamar yadda majiyar ta sanar, da tuni an kashe samarin in ban da 'yan sanda sun bayyana da wuri. Ya kamata ace an tuhumesu akan yadda su kayi, su ka samo 'yan kamfan mata da rigunan nonon da suka saka a akwatin gawar. Ya kamata hukuma ta hukunta su.

KU KARANTA: Hukuncin Ubangiji na bi, na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, Umahi

An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata

An kama matasa biyu dauke da akwatin gawa dankare da rigunan nono da dan kamfai na mata. Hoto daga @TheCableng
Source: Twitter

Jami'in hulda da jama'ar jihar, DSO Onome Onowakpoyeya, ta tabbatar da kamun samarin. A cewarta, ga dukkan alamu tsafi samarin za su yi da kayan, Vanguard ta ruwaito.

Onowakpoyeya ta ce sai da aka takura musu sannan suka bude akwatin gawar, inda suka ga 'yan kamfai da rigunan nonon. Ta ce har yanzu ana cigaba da bincike a kan lamarin.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata

A wani labari na daban, a ranar Juma'a, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce yankin arewa ta tsakiya za su ciyar da kasar nan gaba. A cewar Saraki, yankin ne zai kawo mafita ga Najeriya nan gaba, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda yace, arewa ta tsakiyar tana da ma'adanai masu tarin yawa, wanda hakan zai kawo kudi Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel