Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko

Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko

- Ana zargin wani mutum mazaunin Atlanta da casa Budurwarsa bayan siya mata kayan alatu

- Kamar yadda rahoton ya bayyana, ya zane ta ne saboda kayan da ya siya mata sun yi tsada dayawa

- Ya yi mata dukan fitar da rabon shaidan, bayan nuna takaicinsa a kan kashe mata dumbin dukiya

Ana zargin wani mutum dan Atlanta da yi wa budurwarsa da suka hadu a wata kafar sada zumunta dukan tsiya, bayan sun hadu ido da ido, shafin Linda ikeji.

Ana zargin ya daki budurwar ne, saboda ta zabi abubuwa masu tsada, shiyasa ya daki kudinsa.

Benjamin Francher ya shirya haduwa da Brittany Correri a daren Laraba, 11 ga watan Nuwamba. A ranar haduwarsu ta farko, ya mutunta 'yan uwanta da iyayenta.

Sai dai, da suka fita da daddare, kamar yadda Brittany ta ce, sai al'amarin ya sauya salo, bayan sun yi siyayya, suka zarce masaukin baki da ke Buckhead tare.

KU KARANTA: 2023: Lokacin mulkin Ibo ya yi, Okorocha ya bayyana burinsa na shugabancin kasa

Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko

Matashi ya yi wa budurwa mugun duka tare da yunkurin kasheta a kan kudin da ya kashe mata a fitarsu ta farko. Hoto daga @Lindaikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamnan Kogi ya ziyarci Buhari, ya mika wata muhimmiyar bukatar jiharsa gabansa

"Ya hau ni da duka da naushi ko ta ko ina, ta goshina, fuskata, hanci, baya, ciki, kafafuna, ko ina na jikina, sannan ya saita kaina da bindiga. Yana buguna yana ce min ban cancanci ya kashe min wannan uban kudi ba," a cewar Brittany.

A cewarta, "Na yi tunanin kashe ni zai yi, saboda ya yi ta ja na a kasa yana duka na, sai Allah ya taimakeni wani jami'in tsaro ya ceceni."

Ta fito tana daukansa hotuna, hakan yasa yayi gaggawar hayewa mota, ya gudu. Yanzu haka 'yan sanda suna neman Benjamin a kan laifin cin zarafi, garkuwa da mutane da kuma garkame ta babu gaira babu dalili.

A wani labari na daban, Wata 'yar Najeriya, mai suna Chisara Agoha, ta bayyana yadda ta umarci mijinta da ya mallaka mata filinsa, a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Ta ce ta aiwatar da hakan ne, inda ta sa ya canja sunan mallakar filin, zuwa nata. Inda tace masa matsawar yana so aurensu ya dore, to yayi gaggawar mallaka mata filin nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel