Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai

Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai

- Wani bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka kama wani barawon da dan kamfai

- Barawon ya lallaba cikin wani dakin mata, tare da mai raka shi, wanda shi yake nuna masa hanya

- Mutumin kuwa ya sha duka, inda ya rasa inda zai sa kansa, hakuri kawai yake bayarwa

An kama wani barawon dan kamfan mata, ana tsakiyar fargabar satar kamfai a Najeriya, inda ake zargin tsafi ake yi da shi.

Mutumin ya shiga wani gidan mata, tare da mai raka sa har cikin gidan, The Nation ta wallafa.

Saurayin ya bude wani akwati, yana tsakiyar kwasar wandunan, sai mai su ta damke shi.

Ta rasa abinda za ta yi masa, kawai sai barawon mai karfin hali ya fara bata hakuri.

Take a nan aka gayyaci maza suka fara dukanshi, inda ya sha bakar wahala a hannunsu.

KU KARANTA: Hotunan dan Najeriya da ya garzaya kasar waje ya yi wuff da zukekiyar budurwa sun janyo cece-kuce

Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai

Bidiyon yadda jama'a suka yi wa wani mutum dukan mutuwa a kan satar dan kamfai. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

KU KARANTA: Ba mu samu kudi ko kayan tallafin korona daga Buhari ba, Sanatoci

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya gayyaci Dahiru Buba zuwa masaukin gwamnan da ke Abuja a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2020, Channels TV ta wallafa.

Dahiru Buba, mutumin da yayi tattaki daga jihar Gombe har Abuja don taya murnar nasarar Buhari a 2015, ya samu kayan alatu daga hannun gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

Rahotanni sun nuna yadda Buba ya kwanta asibiti kwanaki sakamakon ciwon kafar da ya fuskanta.

Ciwon kafar da ake zargin tattakin ne yayi sanadinshi, bayan Buba ya fara neman taimako ne gwamnan ya bukaci a kai shi babban asibiti don samun kulawa ta musamman.

Warkewarsa ke da wuya, gwamnan ya gayyaceshi Abuja, inda yayi masa kyauta ta musamman don taimakonsa.

Tsohon, dan karamar hukumar Dukku, wanda dama direba ne, yayi matukar farincikin samun kyauta mai tsoka daga hannun gwamnan a ranar Litinin, inda gwamnan ya bashi dalleliyar mota da kuma naira miliyan 2.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel