Tabbas na yi lalata da jikata, amma ban san ta samu ciki ba, tsoho mai shekaru 70

Tabbas na yi lalata da jikata, amma ban san ta samu ciki ba, tsoho mai shekaru 70

- 'Yan sandan jihar Ogun, sun damki Hunsu Sunday, wani tsoho mai shekaru 70

- Ana zargin Hunsu, da yin lalata da jikarsa, mai shekaru 15, har ya kai ga dirka mata ciki

- Tsohon ya amsa laifinsa, amma a cewarsa, bai san jikar tasa har ta samu ciki ba

Hukumar 'yan sanda da ke jihar Ogun, sun kama wani Hunsu Sunday, mai shekaru 70 bisa zargin dirka wa jikarsa mai shekaru 15 ciki.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sanda, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da aukuwar lamarin, 'yan uwan yarinyar ne suka shaida wa hukuma abinda yake faruwa.

Kamar yadda suka shaidawa 'yan sanda, yarinyar ta koma zama tare da tsohon ne, tun rasuwar mahaifiyarta, The Nation ta wallafa.

Yarinyar ta dade tana sanar da 'yan uwanta yadda kakanta yake danneta yana lalata da ita.

KU KARANTA: Saraki ya umarci biyan wani hadimarsa N100m duk wata yayin da yake gwamna, Tsohon akawun Kwara

Tabbas na yi lalata da jikata, amma ban san ta samu ciki ba, tsoho mai shekaru 70

Tabbas na yi lalata da jikata, amma ban san ta samu ciki ba, tsoho mai shekaru 70. Hoto daga @TheNation
Source: Twitter

KU KARANTA: Gwamna Inuwa ya kai wa wanda ya taka zuwa Abuja wurin Buhari dauki bayan ya koka da ciwon kafa

Bayan sanar da hukuma hakan, DPO din ofishin 'yan sanda na Ado-Odo, SP Michael Arowojeun, ya sanar da jami'ansa, kafin ya tura su kamo tsohon.

Bayan tuhumar tsohon, ya tabbatar da yin lalata da jikarsa, amma a cewarsa, bai san tana da ciki ba. An kai yarinyar asibiti don duba lafiyarta.

Kwamishinan 'yan sandan, CP Edward Awolowo Ajogun, ya umarci a mayar da tsohon zuwa sashin yaki da safarar mutane da cutar da yara na jihar, don a cigaba da bincikarsa kafin a yanke masa hukunci.

A wani labari na daban, dan dagacin wani kauye ya rasa ransa sakamakon rikicin jami'an kwastam da wasu matasa 'yan sumogal a jihar Kebbi., jaridar The Punch ta wallafa.

Rikicin ya hargitse tsakanin jami'an kwastam na Kaduna da suke aiki a jihar Kebbi, da wasu matasa, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel