Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai

- An kama wani fasto mai suna Bishop Elijah Chukwuebuka, da layoyi da dan kamfan mata a jihar Anambra

- Matasan sun yi masa tsirara kuma tumbur suna shirin banka masa wuta, ya kone kowa ya huta

- Ana cikin wannan tirka-tirkar, wasu suka ceceshi, inda suka kai shi fadar sarkin Umunze

Matasa sun kama wani fasto a Umunze da ke jihar Anambra yana tsafi, sun yi masa tsirara sannan suka yi ta zagaya gari da shi a haka.

Fasto, Bishop Elijah Chukwuebuka, wanda shine mai cocin 'God of Light Anointing Ministry', aka kama da wasu kayan tsafi kamar layoyi da guraye har da dan kamfan mata a cikin cocinsa da take Nsogwu, dake Umunze, da misalin karfe 5 na yamma a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba.

Matasa sun yi wa cocin dirar mikiya inda suka yi yunkurin kona faston, wanda aka fi sani da Big Daddy, amma an cece shi da kyar, inda aka tafi da shi fadar sarkin Umunze.

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai. Hoto daga @TJTrueJustice1
Source: Twitter

KU KARANTA: Ana barazana ga rayuwata saboda mutuwar aurena, Tsohuwar matar Sarki

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai. Hoto daga @TJTrueJustice1
Source: Twitter

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai

Hotuna da bidiyon faston da aka yi wa tsirara bayan an kama shi da layu da dan kamfai. Hoto daga @TJTrueJustice
Source: Twitter

KU KARANTA: Budurwa ta bayyana barnar da tayi wa saurayinta bayan ta gano zai auri wata

A wani labari na daban, Hussaina Salisu, 'yar karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna, ta ce cikin yaranta 15, ta haifi guda 13 ita kadai a gida. Ta ce bata taba fuskantar wasu wahalhalu ba yayin haihuwar yaranta ba.

A cewarta, "cikin yarana 15, guda 2 ne kadai na haifa a asibiti."

Matar, mai shekaru 54 ta ce ba za ta shawarci wata mace ta yi kwatankwacin abinda tayi ba, inda tace, "Da ban samu wayewa ba, da yanzu ban tsinci kaina a halin da na ke ba a yanzu."

A cewarta, lokacin da ta haifi yaronta na fari, tana da shekaru 14 a duniya, shekaru fiye da 28 da suka wuce kenan, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel