Zan amince da hukuncin kisa ga masu fyade da kuma garkuwa da mutane - Gwamna Sule

Zan amince da hukuncin kisa ga masu fyade da kuma garkuwa da mutane - Gwamna Sule

- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule yace a shirye ya ke da ya saka hannu a kan dokar kisa ga duk wanda aka kama da laifin fyade da garkuwa da mutane

- A cewarsa, kowacce jiha tana da kalubalen da take fuskanta, matsalolin da jiharsa ke fuskanta sune fyade da garkuwa da mutane

- Ya yi kira ga shugabannin addini, da na gargajiya a kan su yi kokarin wayar da kan iyaye da wadanda aka yi wa fyade don gaggawar sanar da hukuma

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana niyyarsa ta sa hannu a kan dokar kisa ga duk wanda aka kama da laifin fyade da garkuwa da mutane, matsawar 'yan majalisar jiharsa suka zo da dokar.

Ya sanar da hakan ne a wani taro da suka yi don kawo karshen fyade da garkuwa da mutane a jiharsa, Daily Trust ta wallafa.

A cewarsa, "Matsawar 'yan majalisar jiharsa suka bukaci a yi hukuncin kisa ga mai garkuwa da mutane da kuma mai fyade, to tabbas zai sa hannu a kai."

Ya ce, "Kowacce jiha a kasar nan tana da matsalar da ta addabeta, ni dai manyan matsalolin jihata sune fyade da garkuwa da mutane.

"Lokaci yayi da ya kamata a kara tsaurin hukunci ga masu laifin fyade da garkuwa da mutane."

Ya kara da nuna muhimmancinsa bakin shugabannin gargajiya da na addini don wayar da kan iyaye da wadanda aka yi wa fyade don tabbatar da adalci garesu.

Wadanda suka je taron sun yi kira ga mutane da su bayar da cikakken hadin kai ga kungiyoyin da al'amarin ya shafa don yaki da fyade da sauran ta'addanci a jihar.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wadanda ake zargi da kisan fitaccen likitan Kano

Zan amince da hukuncin kisa ga masu fyade da kuma garkuwa da mutane - Gwamna Sule

Zan amince da hukuncin kisa ga masu fyade da kuma garkuwa da mutane - Gwamna Sule. Hoto daga @Dailytrust
Source: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Gwamnoni sun aike muhimmin jan kunne ga shugabannin al'umma

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Kano sun damke wani Sale Yusuf, mazaunin yankin Ana-dariya dake karamar hukumar Tudun-wada dake jihar sakamakon yi wa matar aure fyade a hanyar kauyen Falgore.

Wanda ake zargin yayi amfani da wuka wurin tsoratar da matar kafin yayi mata fyaden, Daily Trust ta wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sanda, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata takarda, ya ce al'amarin ya faru ne mako biyu da suka wuce, a ranar 6 ga watan Oktoban 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel