Muhimmin sakon shugaba Buhari ga masu zanga zanga - Ministan Matasa

Muhimmin sakon shugaba Buhari ga masu zanga zanga - Ministan Matasa

- Buhari ya shawarci matasa da su gudanar da zanga zangarsu cikin lumana, yana mai cewa babu wanda zai iya dakatar da su kan hakan

- Ministan matasa da bunkasa rayuwa, Sunday Dare ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawarsa da Buhari a ranar Litinin

- Minista Dare ya kara da cewa tuni suka fara tattaunawa da matasa domin sanin bukatunsu don gaggauta cika masu su

Ministan matasa da bunkasa rayuwa, Sunday Dare a ranar Litinin ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari, dangane da zanga zangar da ake ci gaba da yi ta kawo karshen SARS.

Bayan kammala ganawar, Ministan ya shaidawa manema labarai cewa shugaban kasa Buhari ya shaida masa cewa ba shi da ta cewa kan matasan da ke zanga zanga.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Dare ya ce Buhari ya shawarci matasa da su tabbata sun gudanar da zanga zangar su cikin luma ba tare da tayar da zaune tsaye ba.

Ministan ya kara da cewa Buhari ya nuna damuwarsa kan yadda a wasu wuraren zanga zangar ke daukar sabon salo na tayar da tarzoma.

KARANTA WANNAN: Hotunan yadda rundunar soji ta cafke masu safarar shinkafa daga shiyyar Kudu maso Ku

Muhimmin sakon shugaba Buhari ga masu zanga zanga - Ministan Matasa
Muhimmin sakon shugaba Buhari ga masu zanga zanga - Ministan Matasa - @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya ce, "Da farko, shugaban kasa ya ce ba shi da jayayya kan zanga zangar da matasa ke yi, kowa yana da 'yancin yin hakan, sai dai, ya zama wajibi a yi zanga zangar cikin lumana.

"Tabbas, ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun tashin tarzoma a wasu wuraren da ake yin zanga zangar.

KARANTA WANNAN: Rundunar soji za ta fara atisayen murmushin kada a fadin Nigeria

"A wajensu, ya zama wajibi a gudanar da zanga zangar cikin lumana. Ya kuma bayar da tabbacin cewa za a hukunta duk wani jamui'in da aka kama da laifin farwa ma su zanga zangar.

"Don haka, shugaban kasa Buhari na ganin cewa 'yanci ne yin zanga zangar ma damar anyi cikin lumana. Ya ce zai duba bukatun masu zanga zangar don daukar mataki.

"Yana da yakinin cewa matasan Nigeria ba su bin doka da oda ne, kuma ya san cewa matasan Nigeria na da mafarkin samun kyayyawar kasa daga shuwagabannin na gari."

Dare ya kara da cewa tuni suka fara tattaunawa da matasa domin sanin bukatunsu don gaggauta cika masu su.

A wani labarin, A ci gaba da dakile laifukan da suka shafi karya tattalin arziki da sauran laifuka makamantan su a shiyyar Kudu maso Kudu, dakarun atisayen SILENT HEAT III ta samu babbar nasara.

A ranar Asabar, dakarun da ke sansanin soji na IBAKA a jiragen su na ruwa sun cafke wani babban jirgi dauke da buhunan shinkafa a hanyar Utan Iyata da aka yi safarar ta daga Kamaru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel