Ribas: An yi wa Baiwar Allah tsirara saboda ta tsallaka gona ta saci rogon makwabta

Ribas: An yi wa Baiwar Allah tsirara saboda ta tsallaka gona ta saci rogon makwabta

- ‘Yan sa-kai sun wulakanta wata mata saboda zargin ta saci rogo a gona

- A dalilin haka aka tube ta, aka rufe mata ido, sannan aka dauke ta hoto

- Yanzu hotunan wannan mata sun karada shafin Facebook da Whatsapp

Wata mata mai shekara 27 da aka bayyana sunanta a matsayin Comfort Eze ta gamu da kunyar Duniya, saboda zargin satar rogo a gonar mutane.

Jaridar Punch ta bayyana cewa dakarun sa-kai da ke aiki a Ovogo, karamar hukumar Enuoha, jihar Ribas, sun kama Comfort Eze, sun yi mata tsirara.

Wannan Baiwar Allah ta fito ta na neman jami’an tsaro su yi ram da wadanda su ka wulakanta ta.

KU KARANTA: Tsautsayi ya rutsa da ango ana murnar biki, ya karya kafafu

Labari ya zo cewa a ranar 15 ga watan Satumba, 2020, shugaban ‘yan sa-kai na yankin Ovogo wadanda aka fi sani da OSPAC, ya kama Miss Eze.

Jami’an sun zargi wannan mata da shiga gonar makwabta, har ta saci rogo. A daliln haka aka yi mata tunbur, sannan aka baza hotunanta a yanar gizo.

Eze ta shaidawa kungiyar lauyoyin mata na Duniya na reshen Fatakwal cewa ‘yan sa-kan sun nemi ta biya N60, 000 a matsayin tarar da aka ci ta na sata.

Bayan ta biya N52, 000 a matsayin beli, sai kuma ‘yan OSPAC su ka nemi danginta su kara biyan wasu N20, 000, Eze ta shaidawa ‘yanuwanta mata.

KU KARANTA: Hadimar Buhari za ta zama Kwamishinar INEC

Ribas: An yi wa Baiwar Allah tsirara saboda ta tsallaka gona ta saci rogon makwabta

Kwamishinan 'Yan Sanda na Ribas Hoto: The Eagle
Source: UGC

“Sun keta mani kaya, su ka kama ni, su ka rufe mani idanu su na yawo da ni; sun ce su na so ne su kashe ni. Su ka dauki hotunana tsirara, su ka sa a Facebook.”

Wannan mata ta ke fadawa jama’a da Pidigin cewa yanzu hotunan sun zagaye ko ina a gari. Wani ya tabbatar da cewa ya ga wadannan hotuna a kafar Whatsapp.

Dazu kun ji cewa Hon. Princess Onuoha ta kawo wani kudiri a majalisa da zai bada damar amfani da wiwi wajen bincike da kuma nazarin kimiyya da kiwon lafiya.

Rahotanni sun ce wannan kudiri da Miriam Onuoha ta gabatar, ya kai matakin sauraro na biyu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel