Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal

Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal

- Wallafar wata mata da ta kunyata mijinta ta zagaye kafar sada zumuntar zamani ta Facebook

- Matar ta sanar da duniya sunan mijinta da karyar tafiyar da yayi mata yaje ya kama Otal yana sharholiyarsa

- Tace aurenta da shi ya kare, kuma tayi wallafar ne don ya gani, ta sanar dashi cewa ta hakura dashi

Wata mata ta tura wa wata mai kula da wata kungiyar ta kafar sada zumuntar zamani ta Facebook sako, wanda ta fallasa mata mijin ta mai suna Felix Ogiri.

Ta ce Felix na hawa wata mota kirar Range Rover.

A cewar ta, yayi ikirarin zai yi tafiya zuwa jihar Delta, amma tana ganinsa cikin gari, kuma tasan Otal din da ya sauka tare da wata mata.

Ta kara da cewa, yaransu na gida saboda yaki biya musu kudin makaranta.

Ta tura sakon zuwa kungiyar ne saboda ta san mijin nata dan kungiyar ne kuma tana so ya gani, a cewarta.

Ta sanar da shi cewa ta hakura dashi, kuma ta fada mishi inda makullin gidansu yake idan ya dawo.

'Yan Najeriya da dama sun yi ta kwasar nishadi da wannan wallafar, tuni suka yada wallafar.

Bayan faruwar lamarin, maza da dama masu suna Felix sun yi ta fitowa suna cewa ba su bane.

KU KARANTA: Bayan musayar wuta, 'yan Boko Haram sun halaka jami'in JTF a Borno

Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal

Matar aure ta wallafa sunan mijinta a kafar sada zumunta a kan karya da yayi mata ya tare da karuwa a otal. Hoto daga Rachael Mel
Source: Facebook

KU KARANTA: Wata mata ta yi alhinin mutuwar karenta tamkar mutum, ta rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya

A wani labari na daban, wata hira tsakanin saurayi da budurwa a kafar sada zumuntar zamani ta WhatsApp tayi ta yawo a yanar gizo. Saurayin, mai suna Stephen da budurwarsa sunyi hira ne akan shirin auren yayarta.

Bayan yayi ta tambayar budurwar ko za ta aureshi na tsawon shekaru 2 amma ta murje ido ta ki. Saurayin bayan ya ga cewa kullum tsufa yake yi, ya nuna lallai ya kosa yayi aure, sai ya sauya akalarsa zuwa yayarta.

A yadda saurayin yace, tunda budurwarsa mai shekaru 24 bata shirya ba, ya tabbatar yayarta mai shekaru 29 a shirye take tayi aure.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel