Sokoto: An gurfanar da matashin da ya baza bidiyon tsiraicin wata budurwa gabannin bikinta

Sokoto: An gurfanar da matashin da ya baza bidiyon tsiraicin wata budurwa gabannin bikinta

- Rundunar yan sanda ta gurfanar da matashin nan da ya ya nadi bidiyon tsaraicin wata budurwa a gabannin aurenta

- Kotun ta bayar da umurnin adana mata saurayin a jiya Litinin, 5 ga watan Oktoba

- An kuma gurfanar da abokansa su uku wadanda ake zargi da tallafa masa wajen baza bidiyon

Rahotanni sun kawo cewa hukumar yan sanda ta gurfanar da matashi nan mai suna, Aminu Hayatu Tafida, wanda ake zargi da nadar bidiyon tsaraicin wata budurwa a Sokoto gabannin bikinta a gaban kotun majistare da.

Ana tuhumar Tafida da aikata laifi, lalata, yada bidiyon alfasha, bata suna da dai sauransu, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

An tattaro cewa kotun wacce ke a birnin Sokoto ta bayar da umurnin tsare mata matashin.

Har ila yau, bayanai sun kawo cewa an tsare matashin sannan aka gurfanar da wasu abokansa uku da ake zargi da taimaka masa, wajen yada wannan hoton bidiyon zuwa ga wanda zai auri yarinyar da kuma a shafukan sada zumunta.

KU KARANTA KUMA: Ondo 2020: Akeredolu ya kara samun karfi yayinda shugaban ZLP da mambobin jam’iyyar suka koma APC

Sokoto: An gurfanar da matashin da ya baza bidiyon tsiraicin wata budurwa gabannin bikinta

Sokoto: An gurfanar da matashin da ya baza bidiyon tsiraicin wata budurwa gabannin bikinta Hoto: @THISDAYLIVE
Source: Twitter

An bayyana sunayen abokan nasa da aka gurafanar a matsayin Umar Abubakar, Mas'ud Abubakar Gidado da kuma Aliyu Shehu Kangiwa.

Sai kuma na biyar dinsu Hafiz Jaafar wanda kawo yanzu bai shiga hannu ba.

Dansandan da ya gabatar da karar, ASP Samuel Sule ya ce laifukan sun sabawa sassa har bakwai na kundin dokar penal code ta jihar Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana

Sai dai dukkanin mutanen hudu sun musanta wadannan zarge-zargen a gaban kotu.

A wani labarin, an kama wani dan shekaru 33, Stepan Dolgikh saboda kashe matarsa mai shekaru 36 da duka a ranar aurensu a kauyen da ke Prokudskoye a kasar Rasha.

Wasu da abin ya faru a idonsu sun ce mijin ya fara dukan matar ne saboda kishin daya daga cikin bakin da suka hallarci bikin daurin auren da aka yi a wani gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel