Mahaifiya ta tozarta diyarta bayan kama ta da tayi a dakin otal da namiji (Bidiyo)

Mahaifiya ta tozarta diyarta bayan kama ta da tayi a dakin otal da namiji (Bidiyo)

- Wata mata 'yar Najeriya ta ci mutuncin diyarta bayan kama ta da tayi da namiji a dakin otal

- A bidiyon wanda ya bazu, an ga mahaifiyar tana dukan diyarta yayin da take janta wajen dakin

- Jama'a da dama sun taru domin fahimtar abinda ke faruwa tsakanin matan biyu

Wani bidiyon da ya bayyana na mahaifiya tana cin mutuncin diyarta da ta kama a dakin otal ya janyo cece-kuce.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, mahaifiyar ta kama diyarta a dakin otal tare da wani namiji.

Bidiyon da shafin Linda Ikeji ya wallafa a shafinsa na Instagram, an ga mahaifiyar tana jan budurwar zuwa kafar bene yayin da take dukanta.

Jama'a da yawa sun yi dandazo domin ganin me ke faruwa da har mahaifiyar ke jan diyar zuwa wajen otal din.

Mahaifiya ta tozarta diyarta bayan kama ta da tayi a dakin otal da namiji (Bidiyo)

Mahaifiya ta tozarta diyarta bayan kama ta da tayi a dakin otal da namiji (Bidiyo). Hoto daga Lindaikejiblogofficial
Source: Instagram

Tabbas bidiyon ya janyo cece-kuce tsakanin samari da 'yan mata. Wasu sun tabbatar da cewa mahaifiyarsu za ta iya yi musu hakan.

Wasu kuwa sun ce hakan ba za ta yiwu ba saboda iyayensu ba masu zafi bane kamar haka.

KU KARANTA: Zukekiyar budurwa ta wallafa hotonta tana neman saurayi, ta ce kada talakan da ya kawo kansa

KU KARANTA: Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square

A wani labari na daban, wata mata yar kasar Zimbabwe na fuskantar tuhumar kashe rai sakamakon hayar 'yan daba su zane yan matan saurayinta.

Rebecca Masawi da 'yan daban da tayi haya guda 3, Zvikomborero Zvikoni, Liberty Guruve da kuma Tendai Dhai suna gaban kotu, akan laifin kinsan kai, garkuwa da mutane da kuma fashi, bayan sun cutar da wata mata har ta mutu.

Kamar yadda takardun kotu suka bayyana, ran Masawi yayi mummunan baci akan wasu 'yan mata dake bibiyar saurayinta, sai wata dabara tazo mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel