Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari

Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari

- Kotun sojoji da ke zama a Maiduguri a ranar Laraba ta yanke wa wani soja hukuncin kora daga aiki da kuma shekaru 5 a gidan yari

- Kofur Aliyu Yakubu ya yi wa matashiyar budurwa fyade kuma yayi yunkurin kasheta a garin Bama da ke Borno

- Matashiyar ta gane sojan kuma dukkan shaidu sun tabbatar shine yayi aika-aikar

Wata kotun rundunar soji da ke zama a Maiduguri jihar Borno a ranar Laraba, ta kori wani soja daga aiki tare da yanke masa hukuncin zaman shekaru 5 a gidan yari.

Sojan mai suna kofur, Aliyu Yakubu an kama shi da laifin yin fyade a ranar 13 ga watan Yulin 2020 kuma an gurfanar da shi a gaban kotun sojin.

Kamar yadda soja mai gabatar da kara ya sanar, Yakubu ya ja yarinya mai shekaru 13 zuwa wani kango a ranar 1 ga watan Yulin 2018 a Bama inda ya ci zarafinta kafin ya yi mata fyade.

Yarinyar ta sanar da kotun cewa, sojan yayi mata fyade ne yayin da ta bar gidan kanwar mahaifiyarta za ta tafi gidansu.

"Ya tambayeni inda zani kuma na sanar masa, daga nan ya ja hannuna yace in bi shi,"lauya Aminu Mairuwa, mai mukamin Kaftin ya sanar kamar yadda yarinyar tace.

"Ya ja ni zuwa wani kango ta bayan tsohuwar gidan yari sannan ya rufe min baki saboda ina ihu.

“Ya fito da wuka tare da yin barazanar kasheni. Bayan ya yi min tsirara sai ya kasa shigata. Daga nan ya tambayeni ko an taba saduwa da ni, amma nace a'a. A take ya shigeni ta karfi.

"Bayan kammala fyaden, ya yi amfani da bulo wurin fasa min kai kuma ya bar ni ban san halin da nake ciki ba," cewar Mairuwa.

Daga bisani jama'a sun ga yarinyar inda aka dauketa zuwa asibiti. Bayan farfadowarta ta sanar da abun da ya faru kuma ta gane sojan.

KU KARANTA: 'Yan Najeriya za su yi alfahari da Buhari a kan kokarinsa a fannin wutar lantarki - Saleh Mamman

Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari

Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari. Hoto daga Premium Times
Source: UGC

KU KARANTA: Nigeria @ 60: Sarauniyar Ingila ta aike wa Buhari da sakon taya murna

A wani labari na daban, rundunar 'yan sanda a jihar Legas ta tsare wani matashi, Solomon Okon, na tsawon wata guda bayan ya yi yunkurin kashe kansa. Solomon ya sha wani sinadari mai guba da niyyar ya kashe kansa saboda ya rasa aikinsa.

Lamarin ya faru ne a cikin watan Agusta bayan an damkawa Solomon takardar sallamarsa daga aiki a wani asibiti mai zaman kansa.

Wani makusancin Solomon ya bayyana cewa jami'an 'yan sanda sun tsare shi kafin daga bisani su gurfanar da shi a gaban kotu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel