Gwamnatin Yobe ta sanar da ranan komawa makaranta

Gwamnatin Yobe ta sanar da ranan komawa makaranta

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bada umurnin bude dukkan makarantun firamare da sakandare ranar 12 ga Oktoba, 2020.

Kwamishanan ilimin jihar, Dr Muhammad Sani Idris a hirar da yayi da jaridar Leadership a Damaturu, ya ce gwamnatin jihar ta yi alhinin kulle makarantun sakamakon bullar cutar Korona.

A cewarsa gwamna Mai Mala Buni ya baiwa ma’aikatar ilimin jihar ta bude dukkan makarantun firamare da sakandare dake jihar ranar 12 ga Oktoba.

Yace: “Ina farin cikin sanar da cewa ranar Litinin, 12 ga Oktoba 2020, za a koma karatu a makarantun firamare da sakandare bayan bata tsawon lokaci.“

Ya tabbatar da cewa ma’aikatar ilimin ta shirya dukkan hanyoyin dakile yaduwar cutar bisa sharrudan da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Ya shawarci iyaye su mayar da hankulansu kan kiwon lafiyan yaransu ta hanyar taimakawa makarantun wajen samar da kayayyakin yakar annobar.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel