Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure

Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure

- An kama wani Charles Nkubi da laifin kashe wani mutumi da ya kama yana lalata da matarsa, a gadon su na sunnah a Uganda

- Al'amarin ya faru ne a wata Unguwa mai suna Kiwalimu, a daren Lahadi, 27 ga watan Satumba

- Mijin ya kama matarsa dare-dare a gadonsu tare da matashin mai karancin shekaru

Yan sanda sun kama wani mutum mai suna Charles Nkubi da laifin kashe wani matashi sakamakon kama shi akan gadon aurensu da matarsa suna cin amanarsa.

Al'amarin da ya faru a Kiwalimu, Wampewo a garin Kasangati da daren 27 na Lahadi ya firgitar da mutane da dama.

An samu labarin cewa, mamacin mai shekaru 20 da yan kai, na kan gado tare da matar mutumin mai suna Nowerina Nassozi da ke da shekaru 32 da haihuwa, lokacin da mijinta, Nkubi mai shekaru 50 ya lallaba cikin dakin yayi ta bugunsa a kai.

Har yanzu ba'a bayyanar da sunan mamacin ba. Mataimakin kakakin rundunar yan sanda, ASO Luke Owoyesigyire, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin 28 ga watan Satumba, ya kuma ce an kama Nkubi da laifin kisa.

KU KARANTA: Kyawawan hotunan auren hadimin Buhari da kyakyawar matarsa

Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure

Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure. Hoto daga Linda Ikeji
Source: UGC

"Wanda ake zargin ya shigo gidansa bayan sanin kwarton yana daki tare da matarsa, ya dauki katuwar sanda yayi ta buga wa mutumin har sai da ya mutu take anan," cewar ASP Owoyesigyire.

Owoyesigyire yace zasu san hukuncin da zasu yanke wa mai laifin idan sun tabbatar yayi kisan da gangan ne ko kuma tsautsayi.

Nkubi ya tabbatar da cewa yayi bugun ne cikin fushi. An dauki sandar da yayi amfani da ita don karin bincike akan al'amarin, a cewar dan sandan.

Har yanzu yan sanda na neman Nassogi. An gano cewa ta gudu ne a lokacin da mijinta yake dukan kwarton nata. An adana gawar a ma'adanar gawawwaki dake Mulago.

KU KARANTA: Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke garin Dutse a jihar Jigawa a ranar Laraba, ta bada umarnin adana mata wani makaho mai shekaru 60 mai suna Muhammad Abdul.

Ana zarginsa da yunkurin yin luwadi da dan jagorarsa, lamarin da yasa aka bukaci adanasa a gidan gyaran hali.

Alkalin kotun majistaren mai suna Akilu Isma'il, wanda ya umarci a adana masa Abdul a gidan gyaran halin, ya dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel