Kawatace kawai - Tsohon minista Fani Kayode ya yi magana a kan hotunansa da Halima Yusuf

Kawatace kawai - Tsohon minista Fani Kayode ya yi magana a kan hotunansa da Halima Yusuf

- Bayyanar hoton tsohon minista Femi Fani Kayode (FFK) tare da wata falleliyar budurwa sun haddasa cece-kuce a dandalin sada zumunta

- Har yanzu FFK bai saki matarsa ta hudu ba duk da sun dade basa zaune tare sakamakon rikicin 'da ya ki ci, ya ki cinyewa' a tsakaninsu

- Tsohon Ministan ya karyata jita-jitar cewa shi da budurwar, Halima Yusuf, suna shirin yin aure

Tsohon ministan harkokin sufurin sama, Femi Fani Kayode (FFK), ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kan cewa yana shirin sake aure duk da har yanzu da sauran rigima tsakaninsa da tsohuwar matarsa da yanzu basa zaune tare.

A ranar Litinin ne tgsohon ministan ya yada wani hotonsa tare da wata kyakyawar budurwa da aka gano cewa sunanta Halima Yusuf.

Gnin hotunan tare da zukekiyar budurwar sun haddasa cece-kuce da yada gulmar cewa FFK na shirin sake yin aure a karo na biyar.

FFK ya yada hotunan ne daidai lokacin da rikicinsa da matarsa ta hudu, Precious Chikwendu, suke kara zafi, wata alama da ke nuna cewa aurensu ya lalace.

Sai dai, da ya ke mayar da martani a kan cecekucen da jama'a ke yi, FFK ya karyata jita-jitar cewa aure zai kara tare da bayyana cewa Halima ''kawatace da ke da kusanci da ni, na yarda da ita.''

"Anata yada jita-jita a dandalin sada zumunta a kan cewa ina shirin sake aure. Wannan karyace zalla.

"Halima Yusuf, budurwar da jama'a suke cewa zan aura, kawatace kawai, tana da kusanci da ni kuma ina matukar ganin girmamata saboda ta na da kima a idona.

DUBA WANNAN: Rochas Okorocha ya bayyana ma su jawowa Buhari zagi a wurin 'yan Najeriya

"Halima, tare da wasu, sun kasance masu kwantar min da hankali a irin wannan lokaci, a saboda haka ina matukar godiya gareta.

"Ina kira ga duk masu yada karyar cewa za mu yi aure su guji aikata hakan," kamar yadda FFK ya rubuta a shafinsa na dandalin sada zumunta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel