Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

- Ma'aikatan tsaro 15 ne suka rasa rayukansu samakon mugun harin da 'yan Boko Haram suka kai wa tawagar Zulum

- Kamar yadda aka gano, akwai sojoji 2, CJTF 4 da kuma 'yan sanda 8 da suka rasa rayukansu sakamakon harin

- Mayakan ta'addancin sun kai wa gwamnan hari tare da tawagarsa ne a tsakanin Monguno da Baga a jihar Borno

Jami'an tsaro 15 suka rasa rayukan su ranar juma'a, 25 ga watan Satumba, sakamakon harin da yan Boko Haram suka kai wa tawagar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Mutane da dama sun ji munanan raunika sakamakon harin da aka kai tsakanin Monguno da Baga.

Yan sanda 8, sojoji 3 da kuma CJTF guda 4 sun rasa rayukansu sakamakon harin, shafin Lina Ikeji ya wallafa.

A ranar lahadi 27 ga watan Satumba, wani kwamandan CJTF, Mu'azu Alhaji Misiya, ya wallafa hotunan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka ji raunuka.

Ya rubuta, "Allah yayi wa zakakuran dakarunmu rahama".

An samu labarin cewa, gwamnan ya bar Maiduguri zai je Baga ranar Juma'a domin shirin dawo da yan gudun hijira gidajensu.

Wannan ne hari na 2 da akayi wa gwamnan a yan kwanakinnan a wuraren Baga.

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum. Hoto daga Musa Alhaji Misiya
Source: Facebook

KU KARANTA: Sanata Marafa ya aurar da diyarsa tare da marayu 13 a Kaduna

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum. Hoto daga Musa Alhaji Misiya
Source: Facebook

KU KARANTA: Adana karfinka domin amfanin wata rana - Matawalle ga matashin da zai yi masa tattaki

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum. Hoto daga Musa Alhaji Misiya
Source: Facebook

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum

Hotunan sojoji, 'yan sanda da jami'an CTJF da 'yan Boko Haram suka ragargaza a tawagar Zulum. Hoto daga Musa Alhaji Misiya
Source: Facebook

A wani labari na daban, wasu mayakan ta'addancin Boko Haram tare da iyalansu sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a Banki.

Kamar yadda hedkwatar tsaro ta wallafa, ta bayyana hotunan mayakan ta'addancin tare da iyalansu da suka mika wuya ga dakarun sojin Najeriya.

Mayakan ta'addancin tare da iyalansu sun mika kansu ne ga bataliya ta 155 da ke Banki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel