Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga da masu garkuwa hudu a Nasarawa da Taraba

Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga da masu garkuwa hudu a Nasarawa da Taraba

- Sojojin Najeriya karkashin Operation Whirl Stroke da na Guards Battalion sun yi nasarar kai hari mabuyar masu garkuwa da masu tada kayan baya

- Yayin harin hadin gwiwar da suka kai, sojojin sun kashe masu garkuwa biyu sun kuma ceto mutum uku a jihar Nasarawa

- Sojojin sun kuma kai sumame mabuyar wasu masu tada kayan baya da ke da alaka ga Gana nan ma sun kashe biyu sun kwato makamai

Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Nasarawa

Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Nasarawa. Hoto @DefenceInfoNG
Source: Twitter

Dakarun sojojin Najeriya ta musamman na Operation Whirl Stroke da Guards Battalion sun samu nasarori a kan miyagu a jihar Nasarawa.

Sojojin biyu yayin wani harin hadin gwiwa da suka kai a ranar 25 ga watan Satumba a kusa da Mararaba Udege a jihar Nasarawa sun kai hari wani wuri da ake zargin mabuyar masu garkuwa ne a hanyar Bakonu da ke karamar hukumar Nasarawa.

DUBA WANNAN: Mutum 20 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

Sun yi nasarar ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su sannan sun sun kashe masu garkuwa da mutane biyu yayin musayar wutan.

Tuni an sada mutanen da aka ceto da iyalansu.

A wani cigaba mai alaka da wannan, bayan samun ingantattun bayanan sirri game da wata matattaran miyagu masu alaka da marigayi Gana, sojoji sun kai hari a kauyen Kwaghaondo a karamar hukumar Chanchanji a karamar hukumar Takuma a Taraba.

Masu tada kayan bayan sun bude wa sojojin wuta amma suka mayar musu nan take kuma daga bisani suka yi galaba a kan miyagun inda suka kashe biyu cikinsu.

KU KARANTA: Hotuna: Obaseki ya kai wa Buhari ziyara bayan kayar da dan takarar APC a zabe

Sojojin sun kwato bindiga AK47 guda daya da alburusai da harsashi masu yawa.

Wannan na cikin wata sanarwar ce da Kakakin hedkwatan tsaro, Manjo Janar John Enenche ya fitar ta shafin Twitter na hukumar a ranar Asabar 26 ga watan Satumba.

Sanarwar ta yi kira ga mutane su cigaba da bawa rundunar hadin kai ta hanyar bada bayannan sirri da zai taimakawa sojojin magance miyagun.

A wani rahoton, an kashe jami'in hukumar 'yan sandan farin kaya, DSS, a daren ranar Laraba yayin musayar wuta tsakanin jami'an tsaro da dilalan bindiga a kauyen Kalong da ke karamar hukumar Shendam ta jihar Plateau.

Daily Trust ta ruwaito cewa sunan jami'in da aka kashe Barista Mukhtar Moddibo dan asalin karamar hukumar Misau daga jihar Bauchi. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel