Bullar cutar Korona ya nuna cewa Allah na fushi da mu - Aisha Buhari

Bullar cutar Korona ya nuna cewa Allah na fushi da mu - Aisha Buhari

- Aisha Buhari ta yi kira da yan Najeriya su koma ga Allah, yana fushi da su

- Ta ce abinda ya sa aka jarrabemu da annobar cutar Korona da ta addabi duniya kenan

Uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Aisha, ta ce bullar annobar cutar Korona ya nuna cewa Allah na fushi da mutanen duniya.

Aisha ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Masallacin kasa dake birnin tarayya Abuja, yayin muhadaran murnan cikar Najeriya shekaru 60 da samun yanci.

Yayinda take kira da a kara kaimi wajen yaki da cutar, ta yi kira ga yan Najeriya su taimakawa kasar da addu'an zaman lafiya da cigaba yayinda ake murnan shekaru 60 da samun yanzin kasar.

"Duniyar nan ta canza sakamakon annobar nan kuma annobar na nuni ga cewa Allah madaukaki yana fushi da mu," Tace.

"Akwai bukatar mu nemi gafara. Ina tunanin bamu da wata mafita da ya wuce neman gafara daga Allah."

KU KARANTA: Da duminsa: Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba

Bullar cutar Korona ya nuna cewa Allah na fushi da mu - Aisha Buhari
Credit: @aishaMbuhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba ginawa jamhuriyyar Nijar layin dogo zamuyi ba - Garba Shehu ya yi fashin baki

A cewar NAN, uwargidan shugaban kasan ta bukaci yan Najeriya su cigaba da goyon bayan kokarin gwamnatin nan na tabbatar da jin dadin yan Najeriya.

"Shugaban kasa ba zai iya shi kadai ba. Yana bukatan goyon baya da hadin kan dukkan yan najeriya, da wadanda ya baiwa mukami," Tace

Wadanda ke hallare a taron sun hada da uwargidar tsohon shugaban kasa, Hajiya Turai Yar'adua; mai baiwa shugaban kasa shawara kan lamuran mata, Hajo Sani; uwargidar tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Mairo Al-Makura da uwargidar tsohon gwamnan Zamfara, Asmau Yari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel