Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarki, bari in karanta tarihin nadin sarki a Zazzau - El-Rufa'i

Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarki, bari in karanta tarihin nadin sarki a Zazzau - El-Rufa'i

- Gwamnan jihar Kaduna na shirye-shiryen zabawa masarautar Zazzau mai tarihi sabon sarki

- El-Rufa'i na bayyana cewa duniya ta zuba ido kan wanda zai zaba

- Ya yi addu'a Allah ya bawa masu zaben sarki a masarautar hikiman zaben na kwarai

Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana wani abin birgewa da yakeyi domin wayar da kasan kafin yiwa masarautar Zazzau zaben sabon sarki bayan rasuwar marigayi Shehu Idris.

Da yammacin Alhamis, gwamna El-Rufa'i ya daura hoton wani littafin tarihi da aka wallafa kan masarautar Zazzau da yadda aka zabi sarakuna a baya.

Littafin wanda bature, M.G Smith, ya wallafa mai suna 'Government in Zazzau' na dauke da yadda salon mulkin masarautar tsakanin shekarar 1800-1950.

El-Rufa'i ya ce yana sake karanta littafin ne domin kara ilimi kafin ya yanke shawara kan wanda zai zaba.

El-Rufai yace: "Yayinda nike sauraron sunaye daga masu zaben sarkin masarautar Zazzau, ina sake karanta littafin Farfesa G Smith kan yadda akayi zaben sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 da zai daura ni kan hanyar zaben na kwarai)."

KU KARANTA: Ba ginawa jamhuriyyar Nijar layin dogo zamuyi ba - Garba Shehu ya yi fashin baki

DUBA NAN: Koriya aikowa Najeriya kyautan rumfar gwajin cutar Korona na zamani

A jiya mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa yana sauraron masu zaben sarki a masarautar Zazzau su gabatar masa da shawarwarinsu kan sabon sarkin da za'a nada.

El-Rufa'i ya bayyana cewa lallai ya lura mutane da dama sun zuba ido kan wanda za'a zaba, kuma saboda haka yayi addu'a Allah ya baiwa masu zaben Sarki hikiman zaban Sarki mai irin dabi'un marigayi Alhaji Shehu Idris.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel