Ba ginawa jamhuriyyar Nijar layin dogo zamuyi ba - Garba Shehu ya yi fashin baki

Ba ginawa jamhuriyyar Nijar layin dogo zamuyi ba - Garba Shehu ya yi fashin baki

- Fadar shugaban kasa ta yi karin bayani kan kwangilar gina layin dogo zuwa Nijar

- Garba Shehu Najeriya za ta ribaci abubuwa da dama idan aka kammala ginin

- Yan kudancin Najeriya sun nuna bacin ransu bisa rashin gina musu ko da guda daya ne

Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya yi fashin baki kan kwangilar ginin layin dogo daga Najeriya zuwa jamhurriyar Nijar da gwamnatinsu ta bada.

Legit ta kawo muku rahoton cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC, ta amince da fitar da Dallar Amurka biliyan 1.95 domin ginin layin dogo da zai tashi daga Kano-Dutse (Jigawa)-Katsina-Jibia zuwa Maradi (Jamhuriyar Nijar).

Ministan Sufuri Rotimi Ameachi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yiwa manema labari jawabi a gidan gwamnati bayan taron Majalisar da Shugaba Buhari ya jagoranta a Abuja.

Ya kuma ce Majalisar ta amince da fitar da Naira biliyan 3 don tsarawa, gini, samarwar da gwajin babban na'urar gyara da daukan kaya mai nauyin ton 150 domin ayyukan gaggawa yayin aikin layin dogon.

Hakan ya janyo cece-kuce cikin yan Najeriya musamman yan bangaren kudancin kasar inda suke zargin shugaba Buhari da bannatar da makudan kudade wajen ginawa jamhurriyar Nija layin dogo amma babu ko daya a kudu.

Amma Garba Shehu ya yi fashin bakin kan lamarin inda yace yarjejeniya akayi tsakanin Najeriya da Nijar domin gina layin dogon.

"A shekarar 2015, an yi yarjejeniya tsakanin Najeriya da Nijar karkashin jagorancin hukumar hadin kai tsakanin Najeriya-Nijar domin ginin layin dogo “Kano-Katsina-Maradi, " Garba Shehu yace.

"Bisa ga yarjejeniya, kasashen biyu zasu gina nasu layin dogo daga cikin kasashensu a hadu a iyaka Maradi."

"Manufar layin dogon shine cin gajiyar ma'adinai, da amfanin gona."

KU KARANTA: Koriya aikowa Najeriya kyautan rumfar gwajin cutar Korona na zamani

Ba ginawa jamhuriyyar Nijar layin dogo zamuyi ba - Garba Shehu ya yi fashin baki

A bangare guda, gwamnatin tarayya a yanzu haka tana ganawa da Kungiyar Kwadago da Kungiyar masu sana'o'i kan barazanar tafiya yajin aikin da kungiyoyin suka yi kan karin kudin lantarki da man fetur.

Ana sa ran gwamnatin tarayyar za ta bayyana tsarin ta na tallafawa al'ummar kasar yayin taron da za ayi a dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel