Fyade a Kano: 'Yan majalisa sun mika bukatar fara yi wa masu fyade dandatsa

Fyade a Kano: 'Yan majalisa sun mika bukatar fara yi wa masu fyade dandatsa

- Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Rano, ya bukaci da a dinga dandake masu fyade a Kano

- Ya bukaci da a sauya dokar 2014 da ta bada damar daure masu fyade na tsawon shekaru goma sha hudu a gidan yari

- Dan majalisar, Nuradden Alhassan Ahmad, ya ce hakan za ta taka rawar gani wurin kawo kasrhen matsalar fyade

Dan majalisar jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Rano, Nuraddeen Alhassan Ahmad, ya bukaci majalisar da ta yi gyaran dokar hukuncin daurin shekaru goma sha hudu a gidan yari ga masu fyade a jihar.

A dokar da aka yi a shekara 2014, an bukaci da a dinga yanke wa masu fyade hukuncin shekaru goma sha hudu a gidan yari, Freedom Radio ta tabbatar.

Dan majalisar ya ce, kamata yayi duk wanda aka kama shi da laifin, a yi dokar da za ta bada damar a yi wa mutun dandaka gaba daya.

KU KARANTA: Zaben Ondo: Kotu ta adana wasu mutum 7 da ake zargin 'yan daban siyasa ne

Fyade a Kano: 'Yan majalisa sun mika bukatar fara yi wa masu fyade dandatsa

Fyade a Kano: 'Yan majalisa sun mika bukatar fara yi wa masu fyade dandatsa. Hoto daga @Saharareporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

A wani labari na daban, a ranar Larabar nan da ta gabata ne Majalisa dokoki ta jihar Kaduna ta amince da yi wa wadanda aka kama da laifin fyade, dandakar mazakuta.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan majalisar jihar sun zauna, sun yi kwaskwarima a kan dokokin fyade. Majalisar dokoki ta yi garambawul a dokar final kwad na shekarar 2017 na jihar Kaduna, wanda hakan ya bada damar shigo da hukuncin dandaka.

Majalisar jihar Kaduna ta bada wannan sanarwa ne a shafinta na sada zumunta na Twitter. Majalisar ta sanar da wannan ne a jiya Alhamis.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, ‘yan majalisar dokokin sun ci ma wannan matsaya ne a zaman da aka yi na ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2020.

“Wannan doka ta bada shawarar a rika yi wa duk wanda aka samu da laifin fyade dandaka a jihar Kaduna.” Majalisar ta rubuta wannan a shafin Twitter.

Daga baya majalisar ta goge wannan magana da ta yi, amma Jaridar The Cable ta ce shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da hakan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel