'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya

'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya

- 'Yan fashi 4 sunyi wa wata mata fyade a gaban mijinta da yaranta a Indiya

- Basu tsaya anan ba, sai da suka kwashe duk wasu kayan alatu dake gidan

- 'Yan sanda sun karyata hakan, sunce maza biyu ne kadai zasu rubuta a takardar rahoto

'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da yaranta a gidansu dake Indiya.

'Yan fashin guda hudu ne suka kai farmakin a wani kauye dake jihar Punjab a Indiya. Wannan abu da 'yan fashin suka yi ya jawo zanga-zanga a kasar.

Fyade dai ya zama tamkar ruwan dare a cikin 'yan shekarun nan a kasar ta Indiya.

Wani jami'in dan sanda yace sai da yan fashin suka bincike gidan tsaf tukunna sukayi wa matar fyade, ka na suka kwashe duk wasu kaya masu tsada dake cikin gidan.

'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya

'Yan fashi sun yiwa wata mata fyade a gaban mijinta da 'ya'yanta a kasar Indiya | Photo credit: Associated Press
Source: Facebook

Sun bar gidan da gwalagwalai na kimanin Rupee 20,000 hakan yayi daidai da naira dubu dari da biyar a kudin Najeriya.

Mijin matar yace da ya kaiwa 'yan sanda kuka akan wannan lamari ya bayyana cewa sun ja masa kunne akan kada ya tada maganar fyaden.

Daga baya ne suka ce zasuyi bincike akan fyaden, duk da haka suka ki amincewa da cewa yan fashi 4 ne sukayi aika-aikan, lallai sai dai su rubuta mutum 2 a takardar rahoto.

KU KARANTA: A shirye nake na biya ko nawa ne domin a cire ni daga cikin fim din 'Yan Shi'a - Yakubu Muhammed

Sai dai wani dan sanda ya musanta zargin kin rubuta rahoton da mijinta yace sunyi, ya ce tun farko sun rubuta.

Ya ce sunanan suna bincike kuma manyan 'yan sanda ke jagorantar binciken.

Matsalar fyade a India ta jawo hankali a fadin duniya tun lokacin da wasu matasa suka taru sukayi wa wata budurwa mai suna Jyoti Singh yar shekara 23 da haihuwa fyade a watan Disambar shekarar 2012.

Singh ta rasu bayan sati biyu da matasa 6 sukayi mata fyade yayin da take cikin mota, tare da wani abokinta wanda sukayi wa mummunan duka.

Dubbannan jama'a sun fita zanga-zanga a cikin birnin Delhi, inda suke cewa laifin gwamnati ne da ta kasa ba wa mata cikakken tsaro.

KU KARANTA: Mawakin Kano da aka yanke wa hukuncin kisa zai iya zuwa har kotun koli - Ganduje

Firaministan kasar Pakistan, Imran Khan yayi kira da a fara yankewa masu yiwa mata fyade hukuncin rataya, ko kuma ayi amfani da guba da za ta saka gabansu ya yanke.

Firaministan ya bayyana hakane bayan an yiwa wata mata fyade ta karfin tsiya a gaban 'ya'yanta, a makon da ya gabata.

Khan yayi wannan bayani ne, a kokarin da yake na gabatar da misali ga wadanda suka yiwa matar fyaden, inda yace zai yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel