Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, ango ya fasa

- Hukumar Hisbah reshen jihar Sokoto ta cafke wasu matasa uku da ake zargi da yada wani bidiyon fyade

- An zargi daya daga cikin matasan, wanda da ne ga fitaccen dan siyasa a jihar, da yi wa yarinyar fyade sannan aka nadi bidiyon

- Sai da ana gab da aurenta, matashin ya saki bidiyon wanda hakan yasa angon ya fasa auren baki daya

Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta kama mutane 3 da ake zargi da watsa bidiyon wani yana lalata da wata yarinya yar shekaru 16 da haihuwa a kafafen sada zumunta.

Da auren yarinyar zai kama 17 ga watan Oktoba,sakamakon yawon da bidiyon yayi an fasa aurenta.

Shugaban hukumar Hisbah na jihar, Adamu Kasarawa, ya sanar da yan jaridu cewa, za'a mika yaron wani dan siyasa na jihar da abokanshi hannun hukuma domin daukan mataki.

Kasarawa yace kungiyar ta gama duk wani bincike a kan lamarin kuma zata tabbatar da yanke hunkunci ga masu laifin.

Mahaifiyar yarinyar wacce aka boye sunanta, tace wanda ake zargin yayi lalata da 'yar ta tun 2017 lokacin tana da shekaru 16 da haihuwa.

Tana tunanin wanda ake zargin ya adana bidiyon ne na tsawon shekaru 3 duk don ya cutar da rayuwar 'yar ta.

KU KARANTA: Gwamna Obaseki ya aike wa da Ize-Iyamu sako mai muhimmanci

Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, Hisbah ta kama su

Matasa 3 sun saki bidiyon fyaden da suka yi wa budurwa ana gab da bikinta, Hisbah ta kama su. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Dubban mazauna Edo sun sha shagali bayan Obaseki ya fito murna a tituna

Kamar yadda ta sanar, an saka ranar auren 'yar ta ya zama 17 ga watan Oktoba wannan shekarar yayin da Baffah ya saki bidiyonsa yana yi wa diyarta fyade.

Ta kara da cewa, wannan mummunan al'amarin yaja an fasa auren 'yar ta, Channels TV ta ruwaito.

Tayi korafi a kan duk yadda tayi kokarin saka hukumar kare hakkin bil adama ta jihar Sokoto a cikin lamarin, hakan ya ci tura.

Mahaifiyar yarinyar tace mahaifin yaron da ake zargi ya tsoratar da ita akan lallai sai ta soke karar amma taki.

Hayatu Tafida, mahaifin yaron da ake zargi, ya tabbatar wa da hukuma cewa yasan maganar amma ya musanta tsoratar da mahaifiyar yarinyar.

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke mabarata 648 a birnin Kano sakamakon zarginsu da take da karya dokokin haramta bara a titunan jihar tun daga watan Fabrairu.

Kakakin rundunar hukumar Hisbah, Lawan Ibrahim, ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a yankunan Bata da ke kan babban titin Murtala Muhammed, asibitin Nasarawa, filin jirgin kasa da kuma wurin Yahuza Suya.

Ibrahim ya ce hukumar za ta ci gaba da kama mabarata wadanda suka ki bin doka a jihar, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel