Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris

Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wakilai domin halartar jana'izar Sarkin Zazzau

- Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya jagoranci wakilan

- Ministocin kudi, muhalli da sufurin jiragen sama tare da Mallam Garba Shehu ne suka halarta

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Lahadi ya shugabanci ministoci da manyan jami'an gwamnati zuwa kasar Zazzau domin wakiltar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wurin jana'izar Sarkin Zazzau.

Daga cikin wakilan akwai ministar kudi, kasafi da tattali, Zainab Ahmed, ministan muhalli, Dr. Mahmud Mohammed da ministan sufurin jirgin sama, Sanata Hadi Sirika.

Hakazalika, daga cikin wakilan shugaban kasan akwai mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu.

Bayan saukar wakilan a makarantar koyon tukin jirgin sama da ke Zaria, wakilan jihar Kaduna wadanda suka samu jagoranci Malam Nasir El-Rufai, suka karbesu.

A yayin mika ta'aziyyar shugaban kasan, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya ce, marigayin Sarkin Zazzau ya bautawa kasa.

KU KARANTA: Zaben Edo: Tattara komatsanka ka bar jihar Edo - 'Yan sanda ga Wike

Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris
Buhari ya tura wakilai Zaria, sun samu halartar jana'izar Sarki Shehu Idris. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zaben Edo: PDP ta yi fallasa, ta zargi APC da yunkurin sauya sakamakon zabe

Ya ce babbar rawar da ya taka wurin gyara da hadin kan 'yan Najeriya ba za a manta da shi ba.

A martaninsa, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce jama'ar jihar Kaduna sun yi babban rashi. Ya mika godiyarsa ga shugaban kasar a kan tura wakilansa da yayi domin halartar jana'izar.

Idan za mu tuna Legit.ng t aruwaito cewa, dabari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng shine rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi. Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau.

Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel