Abubuwan da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Zazzau

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Zazzau

- Allah ya yiwa Sarkin Zazzau, Mai martaba Alhaji Dokta Shehu Idris rasuwa

- Mun kawo maku dan takaitaccen tarihin marigayin

- Ya yi shekaru 45 kenan kan kujerar sarauta kafin Allah ya dauki ransa a yau Lahadi

A yau Lahadi, 20 ga watan Satumba ne aka wayi gari da mummunan labari na rasuwar Sarkin Zazzau, Mai martaba Alhaji Dokta Shehu Idris.

An haifi marigayin ne a watan Maris na shekarar 1936, cikin iyalan Malam Idrisu Auta wanda ake kira Auta Sambo da Hajiya Aminatu.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya tabbatar da mutuwar Sarkin Zazzau, ya sanar da lokacin jana'iza

Kakansa ne Sarkin Zazzau Abdulkarimi wanda ya yi mulki daga 1834 zuwa 1846.

Idris ya fara karatunsa a wajen wasu malaman Islamiyya biyu a Zaria sannan ya ci gaba da karatun Boko a Zaria Elementary School, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya kasance a makarantar daga 1948 har zuwa 1950, a wannan lokacin ne Idris ya rasa mahaifinsa yana da shekaru 12 a duniya.

Idris ya ci gaba da karatun Islamiya da na boko sannan ya shiga makarantar Zaria Middle School a 1950 inda ya kammala karatunsa a 1955.

Daga nan sai ya tafi makarantar kwalejin horar da malamai ba Katsina.

Abubuwan da ya kamata ku sani ame da Marigayi Sarkin Zazzau

Abubuwan da ya kamata ku sani ame da Marigayi Sarkin Zazzau Hoto: Daily Nigerian
Source: Twitter

Daga shekarar 1956, ya koyar a wurare daban-daban a cikin garin Zariya da ƙauyuka. Ya koyar a Zangon Aya, ya koyar a Paki, har ya yi hedimasta a Pakin.

Ya kuma yi hedimasta a Hancin Kare a makarantar 'Town School No.3''.

A shekarar 1962 ya bar aikin malamta inda ya koma karkashin hukumar 'NA' (Native Authority) ta Zariya a zamanin Sarkin Zazzau Aminu.

Ya kuma yi aiki a matsayin jami'in sadarwa na hukumar kula da kananan hukumomi da masarautu na jihar Arewa, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Har ila yau Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya ba shi mukamin Babban sarakatare na musamman na sarki.

Daga nan ne sai aka nada shi sarauta, ya zama wakilin ofis, wato mai daukar nauyin duk abin da ya shafi aikin masarauta a karkashin 'Native Authority' a wannan lokacin.

Ya rike wannan mukami na tsawon kamar shekara biyu zuwa uku, sai Mai Martaba Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu ya nada shi hakimin birni da kewaye, mukamin da ya rike na tsawon shekara biyu zuwa uku, yana hakimi kuma Dan Madamin Zazzau.

KU KARANTA KUMA: Hankalinmu ba zai kwanta ba har sai an fadi sakamakon zaben kananan hukumomi 2 - PDP

Idris ya gaji Sarki Aminu a shekarar 1975.

A ranar 10 ga watan Janairu, 2015 ne yayi bikin cika shekaru 40 kan kujerar sarauta, sannan a ranar 8 ga watan Fabrairun 2020, yayi bikin shekaru 45 a kujerar sarauta.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

A gefe guda, mun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Sarkin ya rasu a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna a ranar Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel