Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya

Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya

- Ɗan majalisar Tarayya Najeriya, Dakta Hassan Usman Sokadabo zai aurar da yaransa guda biyar a rana ɗaya

- Dakta Usman Sokadabo shine ɗan majalisa mai wakiltan yankunan Gwagwalada, Kuje, Kwali da Abaji a birnin tarayyar Abuja

- Ɗan majalisar ya wallafa katin gayyatar a dandalin sada zumunta tare da hotunan kafin aure na biyu daga cikin ƴaƴan da zai aurar

Za a ɗaura auren ƴaƴan ɗan majalisar tarayya Najeriya daga Abuja su biyar a rana ɗaya.

Ƴaƴan na cikinsa sun haɗa da uku maza da kuma guda biyu mata kamar yadda sanarwar da ya wallafa a dandalin sada zumunta ya nuna.

DUBA WANNAN: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya
Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya.
Asali: Facebook

Mahaifin su, Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gwagwalada, Kuje, Kwali da Abaji, Hon. Dakta Hassan Usman Sokadabo ya sanar da hakan a ranar Alhamis 17 ga watan Satumba.

Ya wallafa katin gayyatar ɗaurin auren a dandalin sada zumunta inda ya gayyaci abokai, ƴan uwa da ƴan siyasa zuwa ɗaurin auren.

KU KARANTA: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Za a ɗaura auren ne a ranar 26 ga watan Satumban shekarar 2020 a birnin tarayya, Abuja.

"Ina son amfani da wannan kafar don gayyatar ƴan mazabaɓa ta, abokai, ƴan uwa da ƴan siyasa zuwa ɗaurin auren yara na maza uku da mata biyu da za ayi a ranar 26 ga watan Satumba Insha Allah. Lokutan ɗaura kowanne auren na cikin katin gayyatar da ke ƙasa. Nagode," kamar yadda ya rubuta.

Kawo yanzu dai ɗan majalisar ya wallafa hotunan kafin ɗaurin auren ƴaƴansa mata biyu an angwayensu ne.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta buƙaci hukumomin kula da jin dadin alhazzai na jihohi su fara yin rajistan maniyyata hajji na shekarar 2021.

Kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka, Abdullahi Magaji Harɗawa cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce hukumomin Kula da aikin hajji na Saudiyya ne za su gindaya sharrudan yin aikin hajjin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel