Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja

Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja

- Sakamakon labarin cewa yan Boko Haram na shirin kai hari Abuja, hukumar raya birnin ta fara daukan matakai

- Hukumar ta fara da rusa gidajen karuwai saboda nan ne matattarar yan iska

- Hukumar ta ce asibiti za a gina a wuraren da aka yiwa rusau

Hukumar raya birnin tarayya FCTA, a ranar Laraba, ta fara rusa gidajen karuwai da gidajen da aka gina ba bisa tsari ba a unguwar Daki Biyu, garin Jabi, Abuja.

Diraktan sashen bibiyan ayyukan a FCTA, Mukhtar Galadima, ne ya jagoranci aikin tare da jami'an tsaron gwamnati da yan sa kai, Punch ta ruwaito.

Galadima ya ce an fara rusau din ne saboda matsalar rashin tsaron da ke karuwa a birnin tarayya.

Ya ce dukkan gine-ginen da akayi a filayen gwamnati dake Daki Biyu tuni akwai tsarin ginin da akayi musu.

Ya ce zasu tabbatar da cewa hukumar kiwon lafiyar Abuja ta gina asibiti a kan filin.

Yace, "Mun aiwatar da aikin ne saboda karuwar matsalar tsaro kuma yayin gudanar da rusan, mun gano wasu wukake a wani wuri da ake kira Sambisa. Ana amfani da wukan wajen kashe mutum."

Diraktan ya yi kira ga dukkan wadanda aka baiwa filaye su yi gini a kai ko kuma gwamnati ta kwace.

Sakataren Sarkin Daki biyu, Andy Sanda, ya ce "gaskiya abin da akayi da matukar zafi amma mun hakura saboda ba zamu iya yaki da gwamnati ba."

KU KARANTA: Bayan shekaru 21 a tare, kotu ta raba ma'aurata saboda uwargida ta lashi takobin ba zata sake yiwa miji girki

Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja

Hukumar raya birnin tarayya ta fara rusa gidajen karuwai a Abuja
Source: Facebook

Wannan ya biyo bayan bayanin gwamnatin Najeriya ta cewa yan ta'addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka.

Gwamnatin ta ce yan ta'addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja.

KARANTA WANNAN: Hukumar yan sanda ta tabbatar da harin da aka kaiwa jami'anta a Sokoto (Hotuna)

A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga.

Takardar tace: "Labarin da Kontrola Janar na hukumar Kwastam ya samu ya nuna cewa akwai mabuyan yan ta'addan Boko Haram a ciki da wajen birnin tarayya Abuja."

"Karin bayani ya nuna cewa suna shirin kai hari wasu wurare cikin birnin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel