Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari tsirara a Uganda

Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari tsirara a Uganda

- Kimanin fursunoni 200 ne suka tsere daga wani gidan yari da ke Moroto a arewa maso gabashin kasar Uganda

- Fursunonin sun shiga dakin ajiye makamai sun tube tufafinsu sannan suka bazama cikin daji don shiga wani gari da ke kusa da gidan yarin

- Rundunar sojin kasar ta ce fursunonin sun tube kayansu ne domin kada a gane su kuma ta gargadi mutane su kula domin suna iya shiga gidaje satar kaya

Jami'an tsaro a Uganda sun bazama neman wasu fursunoni fiye da 200 da suka tsere daga gidan yari, sun shiga wurin ajiye makamai sun tube tufafinsu sannan suka bazama cikin daji a arewa maso gabashin kasar.

A kalla mutane uku - daya soja biyu kuma cikin fursunonin - sun mutu yayin musayar wuta da aka yi a cewar kakakin rundunar sojin kasar, Birgediya Flavia Byekwaso.

Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari tsirara a Uganda

Fursunoni 200 sun tsere daga gidan yari tsirara a Uganda. Hoto Aljazeera/Pm News
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin Katsina za ta bawa tubabbun 'yan bindiga gidaje da shaguna da gonaki

Fursunonin sun tsere daga gidan yarin ne a ranar Laraba kusa da barikin sojoji da ke Moroto. "Sun ci galaba a kan direbobin da ke aiki a ranar," in ji Byekwaso.

Fursunonin da suke tsere rukakun masu laifi ne da aka daure saboda laifuka masu alaka da satar shanu a yankin, a cewar ta.

Sun tube tufafinsu domin kada a yi saurin gane su da lauyin ruwan dorowa na kayan gidan yarin sannan suka tsere wurin Dutsen Moroto, wani gari mara mutane sosai a cewar kakakin sojin.

KU KARANTA: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara

"Har yanzu muna cigaba da nemansu," in ji ta, a lokacin da ta ke yi wa mutane gargadin cewa za su iya afkawa gidajen mutane don neman tufafin da za su saka.

Kokarin da aka yi na ji ta bakin hukumomin gidan yarin bai yi wu ba a lokacin hada wannan rahoton kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Dakarun sojojin Najeriya a ranar Litinin sun lalata maɓuyar shugaban masu tayar da ƙayan baya na Benue da aka kashe Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana.

Sun kai sumammen ne a garin Adu da ke Chanchanji a ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel