Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade

- Bayan kammala shirya dokar da majalisa tayi, El-Rufa'i ya katabta hannu

- Za'ayi amfani da salon dandakar zamani yadda Likitoci zasu yi ba tare da amfani da wuka ba

- Hakazalika an samar da doka ga matan da ke yiwa yara maza fyade

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar Penal Code 2020, wacce ta tanadi dokar dandaka ga duk wanda aka kama da laifin fyade a jihar.

A jawabin da gwamnan ya saki a shafinsa ta Tuwita @GovKaduna, ya ce duk mutumin da aka kama ya yiwa wata yarinya ko yaro fyade a jihar zai fuskanci dandaka.

Hakazalika duk macen da aka kama ta yiwa namiji fyade za a cire mata 'indararon mahaifa watau 'Fallopian Tube'.

Wani sashen jawabin yace: "Malam Nasir El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar Penal Code 2020 na jihar Kaduna wacce ta tsaurara hukunci kan fyaden yara, wanda ya hada da dandaka ga maza da kuma cire 'indararon mahaifa watau Fallopian Tube'' ga mata."

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade
Source: Twitter

KU KARANTA: Ana shirin shigo da kaji masu dauke da cutar Korona Najeriya - Hameed Ali, CG Kwastam

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade

Yanzu-yanzu: El-Rufa'i ya rattafa hannu kan dokar dandake mai fyade
Source: Twitter

Ga jerin hukunce-hukuncen da sabuwar dokar da tanada kamar haka:

1. Idan aka samu mutum da laifin aikata fyade a kan yaro ko yarinya 'yan kasa da 14, za a kasheshi bayan an dandakeshi.

2. Hukuncin dandaka da kisa sun wajaba a kan duk wanda aka samu da laifin saduwa da yaro ko yarinya 'yan kasa da shekara 14

3. Idan mace ta yi wa yaro fyade, to za a zartar da hukucin yanke mata wasu indararo guda biyu da ke kai maniyyi zuwa mahaifa (bilateral salpingectomy) sannan a kasheta.

4. Hukuncin dandaka da daurin rai da rai ya hau kan wanda aka samu da laifin aikata fyade ga yaro ko yarinya da suka haura shekara 14.

5. Idan aka samu yaro ko yarinya 'yan kasa da shekara da laifin aikata fyade, za a umarci alkalin alkalai na jiha ya saka sunansa a cikin rijistar masu aikata fyade sannan a sanar tare da wallafawa a labarai

6. Rahoton asibiti ya zama wajibi idan shari'ar fyade ta shafi yara 'yan kasa da shekara 14, kamar yadda Honarabul Kachia ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel