Za a fara rataye masu yiwa mata fyade ko kuma a basu guba a kasar Pakistan

Za a fara rataye masu yiwa mata fyade ko kuma a basu guba a kasar Pakistan

- Firaministan kasar Pakistan ya sha alwashin fara bawa masu yiwa mata fyade guba wacce za ta sanya gabansu ya daina aiki

- Ya bayyana hakane bayan harin da wasu matasa suka kaiwa wata mata suka yi mata fyade a gaban 'ya'yanta

- Bayan sun yi mata fyaden matasan sun kwashewa matar kaya sun gudu

Firaministan kasar Pakistan, Imran Khan yayi kira da a fara yankewa masu yiwa mata fyade hukuncin rataya, ko kuma ayi amfani da guba da za ta saka gabansu ya yanke.

Firaministan ya bayyana hakane bayan an yiwa wata mata fyade ta karfin tsiya a gaban 'ya'yanta, a makon da ya gabata.

Za a fara rataye masu yiwa mata fyade ko kuma a basu guba a kasar Pakistan

Firaministan kasar Pakistan Imran Khan | Source: Facebook
Source: Facebook

Khan yayi wannan bayani ne, a kokarin da yake na gabatar da misali ga wadanda suka yiwa matar fyaden, inda yace zai yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Sai dai kuma yace rataye su zai jawo tarayyar Turai ta hukunta kasar Pakistan, saboda haka zai fi kyau ayi amfani da guba wacce za ta saka gabansu ya daina aiki.

KU KARANTA: Idan har Buhari bai canja takunsa ba nan da 2023 Najeriya za ta zama ba tamu ba - Fani Kayode

Da yake magana a gidan talabijin na kasar Pakistan a ranar Litinin 14 ga watan Satumba, Khan ya ce: "Abinda nake gani shine akwai yadda za a sanya gabansu ya daina aiki, na karanta hakan na faruwa a kasashe da dama na duniya."

Rahoton da Mail Online ta fitar, wannan lamari ya faru a ranar Alhamis da safiyar makon da ya gabata, bayan motar matar ta mutu akan babbar hanya kusa da Lahore, saboda rashin man fetur.

A lokacin da take cikin motar ta, sai ta kulle kofar motar ta kira azo a taimaka mata, sai dai kuma wasu maza sun fasa mata gilashin mota suka fito da ita ta karfin tsiya suka yi mata fyade.

KU KARANTA: PDP ta jinjinawa USA a kan hana masu magudin zaben Kogi da Bayelsa shiga kasar

Bayan sun gama yi mata fyade, sun kuma kwashe mata kaya.

'Yan sanda sun kama mutane 15 a makon da ya gabata, amma ance duka cikinsu babu wanda ke da hannu a wannan fyade.

Tuni dai jami'an tsaron sun bayyana sunayen wasu mutane biyu da ake zargi Shafqat Ali da Abid Malhi.

An kama Shafqat a ranar Litinin, inda 'yan sandan suka bayyana cewa samfuri na DNA nashi yayi daidai da wanda suka samu a wajen da lamarin ya faru, haka kuma shima ya amsa laifinsa.

Shi kuwa wani dattijo mai shekaru 64 mai suna Bassey Archibong da ke gida mai lamba 10 a titin Dipo, yankin Owutu da ke Ikorodu a jihar Legas ya gurfana a gaban kotu.

Ana zargin Archibong da laifin yi wa 'ya'yansa mata har hudu fyade masu shekaru 12 zuwa 20 a duniya, Vanguard ta wallafa.

An gano cewa Archibong ya saba ma'amala muguwa da 'ya'yansa mata tun a 2016. An gurfanar da shi a kan laifuka uku da suka hada da lalata da 'ya'yansa a gaban wata kotun majistare da ke Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel