Hukumar NAPTIP ta na zargin Mai kudi da bata ‘Yan mata 2 a Jihar Kano

Hukumar NAPTIP ta na zargin Mai kudi da bata ‘Yan mata 2 a Jihar Kano

- Jami’an NATPIP sun yi ram da wani Mutumi da ya yi lalata da ‘Yan Mata biyu

- Wannan abu ya faru ne da wani ‘Dan kasuwa da kananan yara a garin Kano

- Wanda ake zargi ya amsa laifinsa, ya ce N1200 ta raba shi da wadannan yara

Jami’an hukumar NAPTIP masu yaki da safarar mutane a Najeriya ta tabbatar da kama wani mai kudi da ake zargi da yin lalata da ‘yan yara a jihar Kano.

Hukumar NAPTIP ta reshen jihar Kano ta bayyana cewa Alhaji Salisu Dala ya na hannunta, kuma ta na zargin shi da bata wasu kananan ‘yan mata su biyu.

Rahoton ya ce wannan mutumi, Salisu Dala wani ‘dan kasuwa ne mai shekaru 53 a garin Kano.

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban hukumar NAPTIP na shiyyar Kano da kewaye, Mista Shehu Umar shi ne ya tabbatar da labarin kama wannan mutumi.

KU KARANTA: Gwamnati ta garkame haramtattun dakunan caca a Kaduna

Jami’ai sun cafke wannan mai kudi ne bayan labarin da su ka samu game da zargin da ake yi masa na lalata da yaran a ranar Juma’a 11 ga watan Satumba, 2020.

Kamar yadda jami’in hukumar yaki da safara da cin zarafin jama’a ya bayyanawa ‘yan jarida, wannan mutumi mai suna Salisu ya amsa laifin nasa da kansa.

Hukumar NAPTIP ta na zargin Mai kudi da bata ‘Yan mata 2 a Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje Hoto: RFI
Source: UGC

“Wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa na cewa ya yi lalata da yara biyu masu shekara 13 da 14.”

“Ya shafe shekaru hudu ya na wannan danyen aiki da ‘yan kananan yara.” Inji Shehu Umar.

Wadannan yara biyu da su ka jawo asirin Salisu Dala ya tonu, su na saida ‘Fura’ da ‘Nono’ da ‘Dambu’ ne a Kano.

KU KARANTA: Tinubu sun ware Miliyan 300 saboda sayen kuri’ar Talakawa a Edo

Wajen neman abin da zai rikesu, su ka fada tarkon wannan ‘dan kasuwa da ake zargin ya keta masu alfarma.

Wannan mutumi ya ce ya ba ‘yan matan N500 da N700 ne domin ya yi amfani da su.

Kwanakin baya kun ji yadda ‘yan Sandan Najeriya su ka kubutar da jarirai 24 daga wani gidan jarirai a Ribas.

Bayan haka, hukumar ta ce ta ceto mutane 134 daga hannun masu safarar mutane a Kano a bana. An kama mutane 86 da ake zargin su na da hannu a wannan aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel