Yadda kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bobiski, ya mutu a hannun 'yan sanda

Yadda kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bobiski, ya mutu a hannun 'yan sanda

- Tun a shekarar da ta gabata, Gwamna Nyesom Wike ya saka kyautar Naira miliyan 30 ga duk wanda ya yi sanadin kama Boboski, fitaccen dan fashi da makami

- A ranar Asabar, jami'an 'yan sanda tare da hadin guiwar 'yan sintiri sun damke dan fashin da makamin wanda ya mutu a hannun 'yan sanda jim kadan

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Ribas, ya sanar da cewa musayar wuta aka yi tsakanin 'yan fashin da jami'an tsaro wanda ya kai ga mutuwar dan uwan Boboski

Bayan shekara daya da Gwamna Nyesom Wike ya sa kyautar Naira miliyan 30 ga duk wanda ya yi sanadin kama fitaccen dan fashi da makami kuma mai garkuwa da mutane, Honest Diigbara, wanda aka fi sani da Boboski, jami'an 'yan sanda sun damke shi.

Amma kuma kamun nashi bai zo da sauki ba, saboda sai da jami'an tsaro da 'yan sintiri a Korokoro da ke karamar hukumar Tai suka yi musayar wuta da shi.

Boboski ya mutu a yayin da yake hedkwatar 'yan sanda ta Fatakwal, tare da dan uwansa wanda shine direbansa kuma ya mutu a take bayan kamasu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Joseph Mukan, ya sanar da kamen Boboski da safiyar Asabar a wani samame da suka kai yankin Ogoni.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce 'yan sanda da 'yan sintiri ne suka kai samamen bayan bibiyarsa da suka yi har zuwa Korokoro.

Bayan isar jami'an tsaro, sun yi musayar wuta inda kaninsa ya mutu a take yayin da Boboski ya samu miyagun raunika.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Makarantar horon hafsoshin 'yan sanda ta saka ranar jarabawar shiga

Yadda kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bobiski, ya mutu a hannun 'yan sanda

Yadda kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bobiski, ya mutu a hannun 'yan sanda. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An garkame zauren majalisar Ondo, an hana 'yan majalisar shiga

Boboski na da alaka da manyan laifuka da aka aikata a yankin. Bayan nemansa da ake yi da kuma kamensa, an adana shi a hedkwatar 'yan sanda da ke titin Mosco a Fatakwal.

Mukan ya ce, "Bayan ganinsu da 'yan sanda, sun fara harbinsu inda suka fara matani. Direbansa kuma dan uwansa ya mutu amma an kama Boboski da ransa.

"Daga cikin miyagun ayyukansu akwai garkuwa da Barista Emelogu, wanda suka kashe bayan karbar kudin fansa, garkuwa da kashe DCO Afam, bayan karbar kudin fansa. da sauransu."

Jami'an rundunar ta 6 da ke sansanin Bori a Fatakwal a shekarar da ta gabata, sun tabbatar da cewa 'yan kungiyar Boboski sun kashe mata jami'i.

Mukan ya kara da bayyana cewa, an alakanta mutuwar wasu 'yan sanda biyu da ke kan babbar hanyar da Boboski.

Har yanzu dai Gwamna Wike bai yi martani a kan kamu da mutuwar Boboski ba.

A wani labari na daban, babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, a ranar Asabar ya bukaci sojojin Opertion Sahel Sanity su ragargaji 'yan bindiga da sauran miyagu ba tare da tausayi ko sassauci ba.

Ya ce rundunar sojojin ba za ta bawa masu aikata laifuka damar su numfasa ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel