Dandaka, kisa, cirema mata indararon mahaifa da sauran hukuncin fyade guda 3 a Kaduna

Dandaka, kisa, cirema mata indararon mahaifa da sauran hukuncin fyade guda 3 a Kaduna

> Majalisar dokokin Kaduna ta yi wa dokar hukunta ma su aikata fyade a jihar garabawul a ranar Laraba

> Sabuwar dokar ta tanadi rukunin hukunce-hukunce a kan duk wani nau'in laifi fyade; a kan mace ko namji, babba ko karami

> Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ne ya nemi majalisar ta yi wa dokar garambawul domin kara tsananin hukunci ga ma su aikata fyade.

A ranar Laraba ne majalisar dokokin jihar Kaduna ta gudanar da garambawul a kan dokokin hukunta wadanda aka samu da laifin aikata a jihar.

Mambobin majalisar sun yi wa dokokin garambawul ne bisa bukatar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i.

A baya majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.

Sai dai, bayan jama'a sun bayyana gazawar hukuncin ta fuskoki da dama, El-Rufa'i ya bukaci majalisar ta yiwa dokar garambawul.

Yanzu sabuwar dokar ta kunshi hukunce-hukunce ga duk nau'ikan laifin fyade; a kan mace ko namji, a kan babba ko karami.

Tanimu Musa Kachia, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Kaduna, ya bayyana hukunce-hukuncen da sabuwar dokar da tanada kamar haka:

Dandaka, kisa, cirema mata indararon mahaifa da sauran hukuncin fyade guda 3 a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna; Malam Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

1. Idan aka samu mutum da laifin aikata fyade a kan yaro ko yarinya 'yan kasa da 14, za a kasheshi bayan an dandakeshi.

2. Hukuncin dandaka da kisa sun wajaba a kan duk wanda aka samu da laifin saduwa da yaro ko yarinya 'yan kasa da shekara 14

3. Idan mace ta yi wa yaro fyade, to za a zartar da hukucin yanke mata wasu indararo guda biyu da ke kai maniyyi zuwa mahaifa (bilateral salpingectomy) sannan a kasheta.

KARANTA: Sabon kwamishinan rundunar 'yan sandan FSARS na kasa ya kama aiki

KARANTA: Bidiyon dumbin makamai da rundunar soji ta kama bayan kashe Gana

4. Hukuncin dandaka da daurin rai da rai ya hau kan wanda aka samu da laifin aikata fyade ga yaro ko yarinya da suka haura shekara 14.

5. Idan aka samu yaro ko yarinya 'yan kasa da shekara da laifin aikata fyade, za a umarci alkalin alkalai na jiha ya saka sunansa a cikin rijistar masu aikata fyade sannan a sanar tare da wallafawa a labarai

6. Rahoton asibiti ya zama wajibi idan shari'ar fyade ta shafi yara 'yan kasa da shekara 14, kamar yadda Honarabul Kachia ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel