Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

- Malamin addinin islama da ke Kano, Nasidi Goron-Dutse ya koka a kan mawuyacin halin rayuwa da musulmi suka shiga a yanzu

- Goron-Dutse ya ce tun da aka hallice shi bai taba ganin al'umma sun shiga irin halin kunci kamar wannan da ake ciki yanzu ba

- Malamin ya yi kira ga masu hali su rika tallafawa gajiyayyu da wadanda ba su da shi domin sadaka ta fi daraja inda aka bawa wanda ke cikin bukata

Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Malami Islama na Kano
Nasidi Goron-Dutse. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

Fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin Kano, Nasidi Goron-Dutse ya koka a kan rayuwar ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki musamman musulmi.

DUBA WANNAN: An kama wani mutum dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgin sama zai tafi Dubai (Hotuna)

Duk da cewa malamin bai ambaci sunan Shugaba Muhammadu Buhari ba, ya nuna damuwarsa a kan yadda wahalhalu, hauhawan farashin kaya da rashin aikin yi ke ƙaruwa a ƙasar.

A cikin gajeren faifan bidiyon malamin da ya yi magana cikin harshen Hausa, ya ce wannan shine lokaci mafi muni da ya taɓa ganin musulmin Najeriya sun shiga.

"A dukkan rayuwa ta, ban taɓa ganin musulmin Najeriya cikin ƙunci wanda ya fi wannan ba.

"Daga halitta ta, da na yi wayo har zuwa yanzu, ban taɓa sanin wani lokaci da musulmi suka shiga wani hali nairin wannan ƙunci, ni ban sani ba," kamar yadda malamin ya koka cikin bidiyon da ake kyautata zaton an ɗauka ne a lokacin da ya ke wa'azi a Kano.

Malami ya cigaba da kira ga al'umma su taimakawa mabuƙata da masu ƙaramin ƙarfi komin ƙanƙantar abinda suke da shi inda ya ce, "babu wani lokaci da taimako ya fi buƙatuwa irin wannan ba".

KU KARANTA: Jaruman matasa 3 da suka ƙwaci kansu daga hannun masu garkuwa a Katsina sun samu kyauta daga gwamnati

Ya cigaba da ƙarin bayani inda ya karanto hadisin Manzon Allah da ke cewa, "mafificiyar sadaka itace wadda aka bawa wanda ke cikin bukata," saboda haka ya yi kira ga masu hali su taimakawa mutane.

A wani labarin daban, kun ji cewa a ƙalla katon ɗin taliya indomie guda 1,958 cikin 3,850 da ya kamata a raba wa mutane a matsayin tallafi a jihar Benue ne yan sanda suka gano an sayar da su a Kano.

Yan sanda sun yi nasarar kama wadanda ke da hannu wurin karkatar da kayan tallafin, an kuma yi holen su tare da wasu da ake zargi da aikata wasu laifukan a ofishin ƴan sanda ta Bompai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel