Macijiya ta gantsari matashi a azzakari sai da ya kusa bakuntan lahira

Macijiya ta gantsari matashi a azzakari sai da ya kusa bakuntan lahira

- Siraphop Masukarat na zaune kan tukunyar ba haya yana kallo a waya yayinda yaji wani abu ta tsikaresa a mazakuta

- Dan matashin bai ankara macijiya ta cijeshi ba sai da ya hangi kanta a cikin tukunyar

- An garzaya da dan shekara 18 din asibiti inda Likitoci suka bada shawaran yi masa dinki a azzakari

Wani matashi a kasar Thailand ya kusa bakuntan lahira yayinda macijiya ta gantsara masa cizo a al'aura yayinda yake ba amfani da ban daki.

Siraphop Masukarat na zaune a bandaki yana kallon bidiyo a wayar hannunsa ranar Talata, 8 ga Satumba, yayinda ya ji wani abu ya tsikaresa a azzakari.

Ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da shi asibiti inda Likitoci suka duba shi.

Yayinda yake hira da Daily Mail kan abinda ya faru, Siraphop ya ce bai gane macijiya ce ta cijeshi ba sai ya ga kanta a cikin tukunyar.

"Ina amfani da bandaki amma bayan dan karamin lokaci, sai na fara jin zafi a azzakari ba. Da na kalli kasa sai na ga macicjiya kan abin zama."

"Kawai kuma sai na ga jini ya mamaye bayin." Ya laburta

Bayan kai shi asibiti, Likitoci sun bada shawaran sai an masa dinki a azzakari.

Hakazalika an wanke masa azzakarin da magungunan kashe dafi.

Macijiya ta gantsari matashi a azzakari sai da ya kusa bakuntan lahira

Macijiya ta gantsari matashi a azzakari sai da ya kusa bakuntan lahira
Source: UGC

Source: Legit

Tags:
Online view pixel