Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki

Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki

- Wani matashi a Nigeria ya labarta yadda mai gyaran magudanar ruwan ban daki ya ciro kwaroron roba 23 a makewayin matar kawunsa

- Ciro kwaroron robar ne ya tilasta kawun na sa ya bukaci ya saki matar, kasancewar bai taba amfani da shi ba tunda ya aure ta

- Matashin ya ce, shekarun kawunsa biyu da auren matar, kuma har sun samu karuwar diya mace

Wani dan Nigeria ya kokawa jama'a bayan da wani mai gyaran fanfon ruwa ya zo gidan sa aiki, domin gyara magudanar ruwan ban dakin kawunsa, ya tsinci kwaroron roba 23 a ciki.

Wannan ya tilasta kawun na sa neman sakin matar, kamar yadda matashin ya bayyana a shafinsa na Twitter.

A cewar matashin, kawunsa da matarsa sun yi murnar shekaru biyu da aurensu da kuma sun samu karuwar diya mace, amma auren na shirin mutuwa saboda ganin kwaroron robar a gidan.

Kawun nasa ya yi mamaki kwarai, kasancewar ba kowane lokaci bane ya ke zama a gida, kuma baya amfani da kwaroron roba idan zai sadu da matarsa.

KARANTA WANNAN: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar wadatar da kasa da abinci

Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki

Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki
Source: Twitter

Matashin wanda ya wallafa labarin a shafin Nairaland ya ce:

"Akwai matsala a cikin gidan! Mun dade muna samun toshewar ban daki a gidan, har sai da aka kira mai gyara ne aka fahimci dalilin toshewar ban dakin.

"Kawuna na da shekaru 44, matarsa kuma 34, sai yarinyarsu guda daya, kuma basu jima da cika shekaru 2 da aure ba. Mafi akasarin lokuta kawuna na zama a shago ne.

"Yana sayar da kayan gyara motoci, bai taba tsammanin matarsa na kawo wani namiji a gidan ba, (wanda ni ta taba gabatar mun da shi a matsayin dan uwan kawun nawa)

"A jiya kawuna ya kira mai gyaran magudanar ruwa domin ya gyara hanyar ruwan makewayin, amma cikin mamaki, sai ga kororon roba guda 23, wani sabo ne har da maniyi a cikinsa.

"Kawuna ya yi mamakin ganin kororon robar matuka, saboda shi bai taba amfani da shi ba tunda ya auri matarsa, ko shekara bai yi da gina gidansa ba," a cewar matashin.

KARANTA WANNAN: Hukumar kwastam ta samu fiye da biliyan ₦9 a cikin wata 8

Matashin ya ce a yanzu dai auren na shirin karewa, kuma yana son matarsa saboda kirkinta, da kuma kokarinta na saya masa wayoyi da rigunan sakawa.

Sai dai ya koka kan yadda ba zai iya yin komai na ganin auren bai rushe ba, tunda ba kowa ne zai ji maganarsa ba, kasancewar karancin shekarunsa.

A wani labarin, Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da 'Kwastam' ta samu rabanu na biliyan ₦976.6 daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2020.

A wata takarda da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa ranar Alhamis, an nuna cewa an samu kudaden ne daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu Najeriya da kudin duti da sauransu.

NAN ta bayyana cewa takardar ta fito ne daga ofishin hulda da jama'a na hukumar kwastam.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel