Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Wasu direbobin motar daukar marasa lafiya sun yi wa budurwa mai shekaru 19 fyade yayin da suka je har gida suka dauketa domin wucewa da ita aisbiti saboda kamuwa da cutar korona da tayi.

An gano cewa, wani matashi ne mai suna Noufal mai shekaru 29 a yayin da suke kan hanyar cibiyar killacewa ta Pathanamthitta da ke yankin Kerala a India, a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba.

An kama Noufal a ranar Lahadi da safe, 6 ga watan Satumban 2020 bayan da wacce lamarin ya faru da ita ta sanar da ma'aikatan asibitin a kan abinda ya faru.

Bayan an kama shi, 'yan sanda sun ce basu ga wani lasisi ko takardar da ta bayyana shi cikin jami'ai ko direbobin motar da aka dauko budurwar ba.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe dan sanda 1, sun raunata wasu hudu

Ministan lafiya na kasar, KK Shailaja, ya kwatanta lamarin da rashin tausayi tare da rashin imani.

Wani jami'i a sashin kiwon lafiya, ya sanar da jaridar The Indian Express cewa ,direba daya kadai ake tura wa dauko marasa lafiya domin gujewa mu'amalar marasa lafiyar da ma'aikatan.

Jami'in ya ce: "Bangaren direban an yi masa shinge kuma babu ma'aikacin lafiya ko na jinya da ke raka direban domin dauko marasa lafiya.

"Ana yin hakan domin karanta yawan jami'an lafiya da za su yi mu'amala da majinyatan. A lokuta kadan ne muke tafiya da ma'aikatan jinya."

Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona. Hoto daga LIB
Source: Getty Images

KU KARANTA: Hotuna: Ma'aikatan da suka yi murabus sun hana shiga da fita a gidan gwamnatin Delta

A wani labari na daban, wani tsoho mai shekaru 67 wanda ya shiga hannun 'yan sanda bayan da ake zarginsa da yi wa yarinya mai shekaru 12 fyade, ya musanta yawan yadda ake ikirarin ya kwanta da ita.

Tsohon ya jaddada cewa sau daya ya taba lalata da ita, amma an ce sau hudu ne bayan babu gaskiya a lamarin, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Tsohon mai suna James Olajoyetan, ana zarginsa da fara lalata da karamar yarinyar tun bayan da ta je hutun babbar sallah wurin kakanta makaho mai zama a yankin Ejigbo a jihar Legas.

'Yan sandan sun zargi Olajoyetan, wanda matukin adaidaita sahu ne, da lalata da yarinyar a dakin kakanta, sannan yana toshe mata baki saboda kada tayi ihun da zai sa kakan nata ya gane.

'Yan sandan yankin Ejigbo sun damke wanda ake zargin a ranar Asabar da ta gabata, bayan da ya kira yarinyar domin ya aiketa amma sai ya fara lalata da ita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel