Zargin Fyade: An shigar da karar kwamishinan albarkatun ruwa, Abdulmumuni Danga

Zargin Fyade: An shigar da karar kwamishinan albarkatun ruwa, Abdulmumuni Danga

An shigar da karar kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kogi, Abdulmumuni Danga, a gaban wata kotun Abuja bisa tuhuramsa da aikata fyade.

Hukumar 'yan sanda ce ta gurfanar da Danga a gaban kotu bisa zarginsa da aikata fyade da cin zalin wata mata mai suna Elizabeth Oyeniyi, wacce ke zaune a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Rundunar 'yan sanda tana tuhumar Danga da aikata laifuka guda 7 wadanda suka hada da fyade da cin zali, an shigar da karar ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A jikin takardar shigar da kara mai dauke da sa hannun ACP Effiong Asuquo, rundunar 'yan sanda ta ce ta gurfanar da Danga ne amadadin gwamnatin tarayya.

An shigar da karar Danga tare da wani mutum guda mai suna Success Omadivi, mai shekaru 35 a duniya.

Daga cikin tuhumar da ake yi wa Danga akwai zarginsa da karyar takardun karatu, yin barazana ga ma'aikacin lafiya, saduwa da Oyeniyi ba tare da amincewarta ba tare da duka da kuma azabtarwa.

Dukkan alifukan sun ci karo da tanadin kundin haramta cin zarafi da musgunawa mutum wanda aka kirkira a shekarar 2015.

Zargin Fyade: An shigar da karar kwamishinan albarkatun ruwa, Abdulmumuni Danga

Abdulmumuni Danga
Source: Twitter

Dangane da batun shigar da karar a Abuja maimakon jihar Kogi, rundunar 'yan sanda ta ce sun yi hakan ne domin bawa Oyeniyi kariya, saboda kar Danga ya yi amfani da siyasa wajen hana shari'a ta gudana cikin sauki.

KARANTA: Ta sa hakori ta gutsirewa mijinta mazakuta saboda ya gaza kashe bera a dakinta

KARANTA: Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

"Mun yi la'akari da dalilan tsaro, shi yasa mu ka ga ya fi dacewa mu shigar da karar a babbar kotun Abuja," kamar yadda 'yar sanda mai gabatar da kara, ACP Effiong Okoh, ta shaidawa kotu.

Oyeniyi ta yi zargin cewa Danga ya ci zarafinta bayan ya yi ma ta fyade fiye da sau daya a ranar 29 ga watan Maris.

Ta shaidawa ACP Okoh cewa Kwamishinan ya wulakantata, ya yi ma ta fyade tare da yin barazanar cewa zai iya kasheta ba don albarkacin danta ba.

Aikata fyade, musamman a kan kananan yara, na neman zama ruwan dare a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel