Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade

Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade

Dangin miji sun kori surukarsu mai suna Ifeyinwa Ezukamma, mai shekaru 40, daga gidan mijinta saboda ta nemi a kwato wa yarta mai shekaru takwas hakkinta bayan wani da ke haya a gidanta ya yi wa yarinyar fyade.

Lamarin ya afku ne a mahaifarsu ya Ogidi, jihar Anambra kamar yadda ta sanarwa manema labarai.

Ta kuma kara da cewar ta kama wanda ake zargin mai shekaru 57 yana aikata ta’asar a ranar 23 ga watan Yuli, kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Ta bayyana cewa tun a watan Maris mutumin ke ta cin zarafin yar tata.

“Na lura da wani hayaniya da motsi a bandaki. Don haka cikin zullumi sai na duba don ganin ko lafiya. Ga mamakina, sai na ga mai haya a gidanmu, wani dattijo yana saduwa da yata,” ta bayyana.

Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade

Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade Hoto: Thisday
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida

Ezukamma ta ce rashin bin gargadin mijinta na cewa kada ta nemi hakkin yar tata ne ya yi sanadiyar da aka kore ta daga gidan auranta.

Kungiyar kare hakkin kananan yara ta kasa da kasa (CRIB), ta ce an kai rahoton lamarin ga ofishinta a ranar 12 ga watan Agusta.

CRIB ta ce za ta tabbatar da ganin cewa an kai wanda ake zargin kotu sannan a hukunta shi.

Jami’in dan sanda na yankin Ogidi, Remigus Ekuri ya tabbatar da lamarin, cewa za a shigar da kara kotu da zaran an samu bayanan likitoci.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza

A wani labarin kuma, yan sandan jihar Bauchi sun kama wani dattijo dan shekaru 50, Yusuf Bako kan aikata fyade ga wata karamar yarinya ‘yar shekaru hudu a duniya.

Bako wanda ke zama a unguwar Yakubu Wanka ya yaudari yarinyar zuwa wani masallaci da ke Aminu Kano inda ya yi mata fyade.

Mai laifin wanda ake zargin kwararren mai fyade ne ya tona laifin da ya aikata a lokacin da yan sanda suka yi masa tambayoyi inda ya kara da cewar an taba kama shi kan wannan laifi a 2001 da 2015 har ya tafi gidan yari.

Ya kuma yi ikirarin cewa yana daga cikin fursunoni da jihar ta yi wa afuwa kwanaki saboda coronavirus.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel