Sau 1 nayi lalata da ita, ba sau 4 bane - Tsohon da yayi wa yarinya fyade

Sau 1 nayi lalata da ita, ba sau 4 bane - Tsohon da yayi wa yarinya fyade

Wani tsoho mai shekaru 67 wanda ya shiga hannun 'yan sanda bayan da ake zarginsa da yi wa yarinya mai shekaru 12 fyade, ya musanta yawan yadda ake ikirarin ya kwanta da ita.

Tsohon ya jaddada cewa sau daya ya taba lalata da ita, amma an ce sau hudu ne bayan babu gaskiya a lamarin, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Tsohon mai suna James Olajoyetan, ana zarginsa da fara lalata da karamar yarinyar tun bayan da ta je hutun babbar sallah wurin kakanta makaho mai zama a yankin Ejigbo a jihar Legas.

'Yan sandan sun zargi Olajoyetan, wanda matukin adaidaita sahu ne, da lalata da yarinyar a dakin kakanta, sannan yana toshe mata baki saboda kada tayi ihun da zai sa kakan nata ya gane.

'Yan sandan yankin Ejigbo sun damke wanda ake zargin a ranar Asabar da ta gabata, bayan da ya kira yarinyar domin ya aiketa amma sai ya fara lalata da ita.

'Yan sandan sun ce yarinyar ta bayyana cewa, "A lokacin da na shiga, sai na tsaya a bakin kofa. Sai yace in shigo ciki domin karbar kudin.

"Shigata babu wuya ya rufe kofa tare da cire min wando sannan ya kwantar da ni a kan gado. Ya cire wandonsa sannan ya fito da mazakutarsa ya kwanta a kaina.

"A yayin da yake yi, na yi kokarin yin ihu amma sai ya dinga dukana yana toshe min baki."

Sau 1 nayi lalata da ita, ba sau 4 bane - Tsohon da yayi wa yarinya fyade

Sau 1 nayi lalata da ita, ba sau 4 bane - Tsohon da yayi wa yarinya fyade. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: FG ba za ta iya cigaba da kashe N5bn a kowanne wata ba a kan 'yan gudun hijira - Majalisa

'Yan sanda a ofishinsu na Ejigbo sun sanar da cewa, kukan yarinyar ya janyo hankalin wani makwabcinsu wanda ya leka ta tagar Olajoyetan, kuma ya balle kofar daga baya inda ya kama shi dumu-dumu yana lalata da ita.

Makwabcin ya fasa ihu wanda ya janyo hankalin mazauna gidan, wadanda suka kama mutumin tare da mika shi hannun 'yan sandan yankin Ejigbo.

Wata majiyar ta sanar da cewa, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa sihiri aka yi masa.

Olajoyetan ya ce, "Na yi fada da wani fasto wanda yace bai amince in daina zuwa cocinsa ba. A watanni shida da suka gabata, ya ce ya yi min wani sihiri wanda babu shakka sai na sha kunya a cikin jama'a.

"Tun daga nan, ban san me ya hau kaina ba. Sun ce sau hudu na yi lalata da ita, amma sau daya ne kadai.

KU KARANTA: Najeriya ta yi rashi, babban basarake a Katsina ya rasu

"A 2005 matata ta rasu, ina da 'ya'ya shida. Babban shekararsa 35 yayin da karamin ke dan shekaru 17. Har yanzu ina mamakin yadda nayi lalata da karamar yarinyar da autana ya girmeta.

"Na bata naira dari amma sai ta rungumeni. A wannan lokacin, hankalina sai yayi mugun tashi."

A lokacin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, bai dauka wayarsa ba kuma bai yi martani ga sakonnin da aka tura masa ba.

A wani labari na daban, wani fitaccen mai fashin na'ura mai kwakwalwa da wayoyi mai suna Tope Oladiran, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Legas bayan fashin da yayi wa wata mata a Ori-Okuta da ke yankin Agric da ke Ikorodu wurin karfe 11 na yamma a ranar 29 ga watan Maris.

Kakakin rundunar 'yan sandan yanki na biyu, DSP Hausa Idris Adamu, ta ce wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyade a gaban 'ya'yanta bayan kammala musu girkin abinci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel