Yadda malami ya ja dalibarsa bandaki, ya nemi yin lalata da ita

Yadda malami ya ja dalibarsa bandaki, ya nemi yin lalata da ita

Gwamnatin jihar Kwara ta gurfanar da wani malamin makaranta a gaban kotu bayan da aka zargesa da yunkurin lalata da dalibarsa mai shekaru bakwai a duniya.

An gano cewa, malamin mai suna Akorede Hammed, ya kai yarinyar cikin bandakin makaranta inda ya yi mata tsirara tare da fara wasa da gabanta, kamar yadda rahoton farko na 'yan sanda ya bayyana.

Bayanin yadda lamarin ya faru yana kunshe a wasikar mahaifin yarinyar wanda ya rubuta a ofishin 'yan sandan yankin da ke Ilorin, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

A wasikar, ya sanar da cewa Hammed ya shiga da yarinyar bandaki, ya garkame kofa sannan ya fara tattabata.

Daga bisani malamin ya bude kofar tare da sakin yarinyar bayan da ta ki amincewa da muguwar bukatarsa.

Binciken 'yan sanda ya nuna cewa, wanda ake zargin shine malamin yarinyar, kuma ya tsere daga makarantar inda ya boye tun bayan aukuwar lamarin.

Daga bisani jami'an 'yan sanda sun damkesa a cikin gari.

Yadda malami ya ja dalibarsa bandaki, ya nemi yin lalata da ita

Yadda malami ya ja dalibarsa bandaki, ya nemi yin lalata da ita. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Dole ne a sake zabar Donald Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden

An maka shi a gaban kotu saboda zarginsa da ake yi da yunkurin lalata da karamar yarinyar wanda ya ci karo da sashi na 285 na dokokin Penal Code.

Amma kuma, an bayyana zaman kotu na farko, alkalin kotun, Lawal, ya dage sauraron shari'ar saboda rashin zuwan wacce lamarin ya faru da ita.

An dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Satumban 2020.

A wani bangare kuwa, matar gwamnan jihar Kwara, Foluke AbdulRazaq, ta bayyana bukatar shiga lamarin kuma ta aike da wakili kotun.

Kungiyar lauyoyi mata ta duniya tare da hukumar rajin kare hakkin dan Adam, ta bayyana a zaman kotun domin ganin yadda za ta kaya.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama masu fyade har mutum 140 a jihar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Sanusi Buba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis lokacin da yayi hira da su.

Ya ce an kama masu laifin a kararraki 87 da aka kai cikin kananan hukumomi 34 na fadin jihar. Kwamishinan ya ce an dauki wadannan rahotanni nasu ne a cikin tsakiyar wannan shekarar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel