Yan sanda sun kama dattijo dan shekaru 50 da ya yi wa karamar yarinya fyade a masallaci

Yan sanda sun kama dattijo dan shekaru 50 da ya yi wa karamar yarinya fyade a masallaci

‘Yan sandan jihar Bauchi sun kama wani dattijo dan shekaru 50, Yusuf Bako kan aikata fyade ga wata karamar yarinya ‘yar shekaru hudu a duniya.

Bako wanda ke zama a unguwar Yakubu Wanka ya yaudari yarinyar zuwa wani masallaci da ke Aminu Kano inda ya yi mata fyade.

Mai laifin wanda ake zargin kwararren fyade ne ya tona laifin da ya aikata a lokacin da yan sanda suka yi masa tambayoyi inda ya kara da cewar an taba kama shi kan wannan laifi a 2001 da 2015 har ya tafi gidan yari.

Ya kuma yi ikirarin cewa yana daga cikin fursunoni da jihar ta yi wa afuwa kwanaki saboda coronavirus.

Da yake taabbatar da kamun Yusuf Bako, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Ahmed Wakili a wani jawabi ga manema labarai a ranar Asabar.

Ya ce tawagar yan sanda ne suka ceto mai laifin bayan fusatattun matasa sun yi masa duka lokacin da suka kama shi yana aikita ta’asar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Yan sanda sun kama dattijo dan shekaru 50 da ya yi wa karamar yarinya fyade a masallaci

Yan sanda sun kama dattijo dan shekaru 50 da ya yi wa karamar yarinya fyade a masallaci Hoto: The Nation
Source: Twitter

Ya kara da cewar wani Jamilu Abdullahi na kwatas din Igbo ne ya ka rahoton daukar doka a hannu da ake aiwatarwa kan Bako a ofishin yan sanda.

Jawabin ya zo kamar haka: “A ranar 03/09/2020 wani Jamilu Abdullahi na kwatas din Igbo ya kai rahoto ofishin yan sanda cewa a wannan rana fusatattun matasa sun yi wa wani mutum duka a unguwar Aminu, sai wasu tawagar yan sanda suka tafi wajen sannan suka ceto mutum da munanan raunuka daban-daban sannan aka kai shi asibiti domin samu kulawa.

"An bayyana sunansa a matsayin Yusuf Bako mai shekaru 50 na unguwar Yakubu Wanka Bauchi. Ya yaudari yarinya yar shekara 4 zuwa wani masallaci a unguwar Aminu sannan ya yi mata fyade.

KU KARANTA KUMA: Mun kashe N31 biliyan cikin watanni 4 don yaki da korona – Gwamnatin tarayya

“Lokacin da aka tambaye shi, ya bayyana cewa an taba kama shi sannan aka tura shi gidan yari sabodaa wannan laifi a 2001 da 2015. Ya kuma yi ikirarin cewa yana cikin fursunonin da jihar ta yi wa afuwa saboda annobar korona.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel