Kano: Ina samun a kalla kwastomomi 200 a kowacce rana - Mai bada aron tufafi

Kano: Ina samun a kalla kwastomomi 200 a kowacce rana - Mai bada aron tufafi

Da yawa daga cikin manyan 'yan kasuwa sun yi nasara ne bayan da suka fara kasuwancin da ba kowa zai dauka hatsarin da suka dauka ba. Daga nan suka kafu har suka yi nasara.

Sun yadda cewa wannan hatsarin da suka shigewa ba tare da tunanin za a iya faduwa ba ne yake kai musu riba.

Ta yuwauwannan ne dalilin da yasa matashi Ibrahim Bature Yakubu ya fara sana'ar bada aron tufafi a birnin Kano.

Wani matashi mazaunin kwatas ta Sani Mainagge da ke birnin Kano da ke cikin shekarunsa na asihrin da doriya, ya ce da yawa daga cikin 'yan uwansa basu yadda da cewa wannan kasuwancin nasa zai haifar da da mai ido ba.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Fansar Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa A Adamawa

Yakubu, wanda yace ya fara kasuwancinsa da sana'ar dinki, ya yi bayanin cewa, "Wasu lokutan na kan dinka wa kaina kaya masu kyau. Abokai kan zo su ara domin zuwa taron kece raini, amma kuma abun na damuna.

"Daga haka ne na mayar da aron na kudi. Daga haka wannan kasuwancin nawa ya fara."

Yanayin tufafin da yake bada aro sun hada da Shadda, huluna da takalman maza, leshi da atamfofin mata. Kudinsu na kamawa daga N500 zuwa N4,500

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kudin aron shadda na kamawa daga N1,500, N3,000 har zuwa N4,500. Na yadin maza yana kamawa daga N500, N2,500, sai kuma atamfar mata N2,000 da kuma leshi N1,500.

Kano: Ina samun a kalla kwastomomi 200 a kowacce rana - Mai bada aron tufafi
Kano: Ina samun a kalla kwastomomi 200 a kowacce rana - Mai bada aron tufafi. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutum mafi muni a fadin duniya ya aura mata ta 3 (Hotuna)

Yakubu ya ce masu kara masa karfin guiwa a wannan sana'ar ta shi, sune matasan da ke son yin shigar alfarma domin halartar bikin aure ko kuma liyafa amma basu da kudin dinka sabbbin kaya.

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Kawo Dalilin Goyon Bayan CBN Kan Buga Sabon Kudi

Duk da Yakubu bai dade da fara wannan sana'ar ba, ya ce yana samun a kalla kwastomomi 200 da ke kiransa a kowacce rana domin magana kan aron kaya, takalma ko huluna.

Ya ce, "Na fara wannan kasuwanci a wata daya da ya gabata. Duk da daga gida kawai nake yi kuma da farko ban so mutane su gane ba. Amma a makon da ya gabata na tallata sana'ar.

"Tun daga wannan lokacin wayata bata huta ba. Wani lokacin da kyar nake samu in yi bacci."

Yakubu ya ce, ya fara kasuwancin a yankinsa ga wadanda ya sani kafin yanzu ya bayyana ga jama'a.

Ya yi bayanin cewa, "A lokacin da na fara, hatta 'yan gidanmu gani suke na haukace da na kirkiro da wannan dabara.

"Wasu cewa suka yi na fara shaye-shaye. Da farko har na fara tunanin barin sana'ar. Alhamdulillah yanzu sun fahimta kuma har albarka suke saka mana."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashi ya kera mota 'Bugatti' daga tarkacen shara, an ga lokacin da ya tuka ta

A kan yadda yake bai wa wadanda bai sani ba tufafin aron, matashin dan kasuwar ya ce yana da dabaru kala-kala.

Ya ce, "ga wadanda ke son aron kaya daga nesa kuma ban sansu ba, suna yin rijista ne da katin bankinsu, katin dan kasa ko kuma duk wata shaida ingantacciya.

"Kun san kasuwanci cike yake da hatsari. Wasu za su iya karba su ki dawowa da kayan, shiyasa muke karbar duk wata shaida gamsasshiya.

"Mu kan ja kunnen masu aron tufafin a kan cewa kada su bata ko su yaga. Duk wanda ya yaga zai siyo mana sabo. Idan ka saka abu mara fita za ka biya kudin wanki N500."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za su iya faruwa idan CBN ya buga sababbin N200, N500 da N1000

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel