Rundunar NDLEA ta yi babban kamun kwaya a Kano

Rundunar NDLEA ta yi babban kamun kwaya a Kano

Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta sanar da samun nasarar kama wata babbar mota da ta shigo da myagun kwayoyi zuwa jihar Kano.

Shugaban hukumar NDLEA shiyyar Kano, Dakta Ibrahim Abdul, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da wakilin gidan radiyon Freedom da ke Kano.

Dakta Abdul ya bayyana cewa sun yi shiri na musamman domin kama motar bayan samun sahihan bayanan sirri a kan shigowar motar Kano.

Ya kara da cewa sun biyo motar tun daga titin shigowa Kano daga Zaria bayan samun bayanin cewa an cakuda miyagun kwayoyi a cikin magungunan da motar ta dauko zuwa Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel