Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kama masu yiwa mata fyade 140 a jihar Katsina

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kama masu yiwa mata fyade 140 a jihar Katsina

- Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama masu fyade 140 a fadin jihar

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Sanusi Buba shine ya bayyana haka ga manema labarai

- Inda ya ce rundunar su ta hada kai da malaman addini, sarakunan gargajiya. iyaye da sauran masu ruwa da tsaki wajen kawo karshen ta'addanci a jihar

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama masu fyade har mutum 140 a jihar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Sanusi Buba, shine ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis lokacin da yayi hira da su.

Ya ce an kama masu laifin a kararraki 87 da aka kai cikin kananan hukumomi 34 na fadin jihar.

Kwamishinan ya ce an dauki wadannan rahotanni nasu ne a cikin tsakiyar wannan shekarar.

Mr Buba ya ce duka masu laifin an kai su gaban kotu domin ta yanke musu hukunci domin ya zama izina ga wasu.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kama masu yiwa mata fyade 140 a jihar Katsina

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An kama masu yiwa mata fyade 140 a jihar Katsina
Source: Facebook

A cewar shi, 'yan sanda suna hada kai da shugabannin addini da kuma shugabannin gargajiya, tare da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki akan yadda za a kawo karshen wannan matsala ta fyade.

Haka kuma ya roki kafafen sadarwa da kungiyoyin kare hakkin dan adam akan su hada karfi da karfe da 'yan sanda wajen yaki da fyade da sauran abubuwa na cin zarafi.

KU KARANTA: Budurwa ta kashe saurayin da yayi mata ciki, bayan ta bukaci ya biyata kudi ya ki

Mr Buba ya kuma yabawa sauran hukumomin tsaro akan goyon bayan da suka bayar wajen yaki da ta'addanci a jihar dama kasa baki daya.

Kwamishinan 'ya bukaci jama'a da su cigaba da bawa 'yan sanda hadin kai wajen kai rahoto akan duk wani abu na ta'addanci domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma baki daya.

Haka kuma Legit.ng ta kawo muku rahoton wani mutumi da wani magidanci ya kira domin ya taya shi ladabtar da danshi da yake sata yaki dainawa ya zaro wuka ya cakawa dan ya fadi ya mutu, saboda yaron yaki bayar da hadin kai.

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama wani mai suna Felix Ezike, mai shekaru 27, da laifin cakawa wani matashi dan shekara 19 mai suna Deji Animashaun wuka, inda tayi sanadiyyar mutuwar shi a yankin Egbe dake Ikotun, cikin jihar Legas.

A cewar rahoton 'yan sandan, mahaifin Deji, Dada Animashaun, ya gayyaci Felix gidanshi domin ya taimaka masa wajen ladabtar da danshi wanda aka kama yana sata kuma yaki canja halinshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel