Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da ya yanke wa budurwa nonuwa a otal (Hotuna)

Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da ya yanke wa budurwa nonuwa a otal (Hotuna)

Wani mutum mai shekaru 41 mai suna Ogbonna Nwankwo, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Anambra a kan zarginsa da ake yi da yunkurin kashe wata mata mai suna Bella Joseph tare da cire mata nonuwa a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba.

A yayin bayani ga manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya ce Ogbonna ya kai Bella otal din Dollar Inn Motel da ke Ihite a karamar hukumar Orumba ta kudu.

Ya ce a yayin da suka shiga dakin otal din, wanda ake zargin ya yi amfani da wuka inda ya sokawa Bella kuma ya fara yunkurin cire mata nonuwa.

Ihun neman taimakon da ta fara yi ne ya janyo hankalin manajan otal din wanda ya gaggauta zuwa dakin.

Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da yake yanka wata mata domin tsafi

Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da yake yanka wata mata domin tsafi. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

KU KARANTA: Zakakuran sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga, sun halaka 4 a Kaduna (Hotuna)

"Ana zargin wani mutum da yunkurin kashe wata budurwa a cikin dakin otal ta hanyar soka mata wuka tare da yunkurin cire mata nononta na dama.

"Ana zargin ya yi wannan yunkurin ne domin tsafi da matar kafin ta yi ihu, inda ta samu taimako daga manajan otal din."

Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da yake yanka wata mata domin tsafi

Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da yake yanka wata mata domin tsafi. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Source: Twitter

Haruna ya ce, jami'an 'yan sanda da ke yankin Umunze sun samu kiran gaggawa inda suka mika budurwar asibitin kwararru da ke Nnewi inda take samun taimakon likitoci.

Ya kara da cewa, jama'a sun kusan kashe wanda ake zargin sakamakon mugun dukan da ya sha kafin zuwan 'yan sandan.

Ya ce wukar mai dauke da jini an sameta a wurin, kuma an ajiyeta a matsayin shaida.

Haruna ya ce lamarin yana hannun sashen binciken manyan laifuka na 'yan sandan domin bincike tare da gano abinda ke tattare da lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel