Yanzu-yanzu: An kara farashin litan man fetur a Najeriya, ya koma N151.1 ga lita
1 - tsawon mintuna
Farashin man fetur ya karu zuwa N151.1 ga lita, a cewar kamfanin kasuwancin man fetur PPMC, wani sashen kamfanin man feturin Najeriya NNPC.
A takardar da jaridar Vanguard ta bayyana cewa ta samu gani, D.O Abalaka na kamfanin PPMC yace: "Ku sani cewa mun daura sabon farashin mai a shafin rubuta kudi."
"A yanzu, farashin man fetur PMS zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida ga lita."
"Za'a fara aiki da sabon farashin daga 2 ga Satumba, 2020."

Asali: UGC
Asali: Legit.ng